Mazauna karamar hukumar Dala da ke jihar Kano, na ci gaba da zama a cikin fargaba, biyo bayan hare-haren da ‘yan daba ke kai wa sama da kwanaki shida da suka wuce.
Zababben dan majalisar dokokin Jihar Kano a jam’iyyar NNPP da ke waklitar mazabar, Lawan Hussaini Dala ne, ya bayyana hakan bayan da ya gabatar da kuduri a wani karamin zaman da majalisar ta yi a jiya Litinin.
- An Bai Wa Iyalin ‘Yansandan Da Suka Mutu A Bakin Aiki Cakin 23m A Zamfara
- Da Dumi-Dumi: Kotun Shari’ar Musulunci Ta Tura Sheikh Idris Abdul’aziz Gidan Yari
Ya ce, unguwannin da abin ya shafa a yanzu na fuskantar kalubale, ganin cewa, ‘yan daban na zuwa kai harin a kullum, musamman ganin cewa suna sace kayan mazuna unguwannin da saran wasu da kuma lalata kayansu.
Lawan wanda kuma shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar ya sanar da cewa, ya gabatar da kudurin ne don janyo hankalin gwamnatin jihar don ta umarci kwamishin ‘yansandan jihar ya tura jami’ansa da kawo karshen matalsar.
Ya ce, unguwannin da abin ya shafa sun hada da Dala, Madigawa, Yalwa, Rijiya Biyu, Adakawa da Dogon Nama, inda ya sanar da cewa, wasu daga cikin mazaunan unguwannin sun yi kaura.
Ya kara a cewa, hare-haren har ya janyo wasu sun rasa rayukansu inda ya kara da cewa, a yanzu haka masu kasuwanci na rufe shagunansu da misalin karfe 7 na dare.
Mataimakin shugaban majalisar Bello Butu-Butu, ya goyi bayan kudurin da Lawan ya gabatar, inda ya ce akwai bukatar a yi garanbawul ga lamarin tsaro na jihar
Bayan majalisar ta amince da kudurin ta dage zamanta zuwa yau Talata.