Masu bibiyarmu a wannan shafi na Ado Da Kwalliya barkan mu da warhaka, barka da sake haduwa a wannan makon.
Duk lokacin da aka yi zancen farin ido ko mai hade da jajajaja galibin ‘yan’uwa mata sukan yi sha’awar a ce suna da shi saboda alama ce ta koshin lafiya da kuma abin da ake son gani a wurin ‘ya mace.
- Zabtare Dala Miliyan 418 A Bashin Paris Club: Gwamnoni Sun Mayar Wa Malami Martani
- Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak
Yayin da ake kara girma, idanunmu kan sauya su ma, ba wai kawai wurin amfanin da suke mana ba har da yanayin kalarsu. Wasu za a ga idanunsu sun yi fatsi-fatsi, wasu rawaya-rawaya wasu kuma kan yi shudu-shudi.
Akan samu haka daga gado na iyaye da kakanni wasu kuma sanadin wani ciwo ne. A zahiri wasu ba su ba da kyawawan kulawa ga idanunsu, wasu kuma ba ma su yi kwata-kwata.
Idan idanu suna samun kyakkyawan kulawa, za a same su cikin koshin lafiya koyaushe. Abubuwa 5 da ke sa ido fari:
- Kokwamba Wannan nau’in abinci an san shi da yawan ruwa a cikinsa, shi ya sa yake da karfi wajen taimaka wa gyara kalar ido ya zama fari. Har ila yau yana taimakawa wajen rage wani bakin kala da ake gani a ido musamman idan mutum ya gaji tibis. Idan kuna neman wani abu cikin sauki da ke sa ido fari, to ku rungumi amfani da kokwamba.
- Sanya wani abu mai sanyi a ido Amfani da wani abu mai sanyi a ido ba kawai yana taimakawa wajen kawar da kumburin ido ba ne, har ma yakan taimaka wajen mayar da ido ya zama fari. A rika tsoma tawul a ruwan sanyi ana matsawa a ido ko kuma a daura kankara a idon, za a sha mamaki. Idan aka rika matsa idon na tsawon minti 5 zuwa 10 na abin da aka sa mai sanyi na wasu lokuta a yini, ido zai yi fari abin sha’awa.
- Samun isasshen bacci na sa ido ya yi fari Samun isasshen bacci a kowane dare kamar na tsawon awa 7 zuwa 8 a kullum yana hutar da jijiyoyin idanu tare da dawo wa idon da kalar farin da yake da ita ta ainihi. Domin kara samun hutu yadda ya kamata da kuma mayar da farin ido, muna ba da shawara a rika wanka kafin a yi bacci.
- Amfani da ganyen shayi Ganyen shayi walau baki ko kore yana taka muhimmiyar rawa wajen sa hutu da kuma kara ingancin lafiyar ido. Idan ana amfani da ganyen shayi, idanu ba za su tsufa da wuri ba. Ganyen shayi na da matukar amfani wajen yaki da kwayoyin cututtuka da kuma abubuwan da ka iya sa idanu su yi ja.
- Yawaita shan kayan marmari da ganyayyaki Cin ganyayyaki na da matukar amfani wajen inganta lafiyar ido da kara masa fari. Haka nan shan kayan marmari.
Ko baya ga amfanin da kayan marmari da ganyayyaki ke yi ga ido, har ila yau sukan kuma taimaka wajen inganta lafiyar hanta da samun sinadarai masu amfani a jiki.