A daren yau Lahadi, da misalin ƙarfe 8:00 na dare agogon Nijeriya, ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Chelsea da Paris Saint-Germain (PSG) za su kara a wasa na ƙarshe na gasar Kofin Duniya na ƙungiyoyin, a filin wasa na MetLife Stadium da ke New Jersey, Amurka.
1. Hanyar da Ƙungiyoyin Suka Bi Zuwa Wasan Ƙarshe
PSG ta lallasa Real Madrid da ci mai ban mamaki 4-0 a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da Chelsea ta doke Fluminense da ci 2-0. Hakan ya kai su zuwa wasan maraka.
- Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Wasan Ƙarshe Tsakanin Chelsea Da PSG
- Kofin Duniya: Real Madrid Za Ta Fara Da PSG A Semi Final
2. Tarihin Haɗin Kai Tsakaninsu
Sun fafata sau 9 a baya, inda PSG ta fi samun galaba da nasara sau 3, Chelsea ta ci sau 2, sannan aka yi kunnen doki har sau 4. Wasan ƙarshe da suka kara shi ne a gasar Zakarun Turai ta 2015/2016, inda PSG ta doke Chelsea 2-1.
3. Girman Lambar Yabo da Za a Baiwa Zakaran Gasar
Ƙungiyar da ta lashe kofin za ta samu fam miliyan 97 daga hukumar FIFA. Hakanan, za ta sanya tambarin kofin na tsawon shekaru 4, sabanin shekara 1 da ake yi a baya.
4. Muhimmancin Wasan ga Duka Kungiyoyin
Ga PSG, wannan kofi na iya zama jaddawalin nasarar su bayan barin Kylian Mbappé. Ga Chelsea kuma, nasarar na iya maido da su sahun gaba a turai da duniya gaba daya.
5. Kallon Duniya na Kan Wasan
Wasan zai jawo hankalin masu sha’awar kwallon kafa a duniya, musamman ganin yadda kowanne ɓangare ke dauke da fitattun ‘yan wasa da kocin da ke ƙoƙarin kafa tarihi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp