An so ga duk wanda zai shiga garin Makka ya yi wanka da niyyar shiga garin. Bayan wankan da mai Hajji ko Umura ya yi na daura Harami, an so idan zai shiga Makka ya yi wani wankan, amma ba dole ba ne.
An so ga wanda zai shiga Makka ya kwana a wurin da ake ce ma Ziduwan saboda Annabi (SAW) da ya zo, ya kwana a nan. Ana so mutum idan zai shiga garin, ya shiga ta saman Makka (da yake garin kamar tudu da kwari ne).
Ana so idan mutum ya shiga Makka bayan ya ajiye kayansa a amintaccen masauki, ya yi gaggawan zuwa Harami. Ya shigo ta Babus Salam (a da; nan ne Babub Bani Shaiba take, sannan da ka shigo ga kofar Ka’aba nan). Idan za a shiga, a tabbatar da yin kankan da kai ga Allah kuma a karanta wannan addu’ar, “A’uzu billahil aziym, wa bi wajhihil kariym, wa suldanihil kadiym minas shaidanir rajiym bismillahir rahmanir rahim, bismillah, allahumma salli ala Muhammadin wa alihi wa sallim, allahumma agfirliy zunubi, waftahali abwaba rahmatika”.
Ma’anar addu’ar ita ce, “Allah ina neman tsari da kai, ya Ubangiji maigirma, da hasken fuskarka (yadda ya dace da shi) maigirma, da sarautarka dauwamammiya, daga shaidani abin jefewa, da sunanka Allah, Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad (SAW) da ‘ya’yan gidansa, ka yi aminci a gare shi. Allah ka gafarta mun zunubina, Allah ka bude mun kofofin rahamarka.”
Ba a Harami ba kawai, a kowane Masallaci an so a karanta daga kan salatin Annabin nan zuwa karshen addu’ar idan za a shiga.
Idan mutum bai iya wannan addu’ar ba, ya yi a’uziyya da bisimillah da salatin Annabi (SAW) da kuma addu’ar da ya iya.
Ana so da zarar mutum ya shiga idanunsa sun kalli Dakin Ka’aba, ya daga hannu ya nuna Dakin ya ce “Allahumma zid haazhal baita tashriyfan wa ta’aziyman wa takriyman wa mahaabatan wa zid man sharrafahu wa karramahu min man hajjahu awi’itamarahu tashriyfan wa takriyman wa ta’aziyman wa birran, Allahumma antas salamu wa minkas salamu fahayyina rabbana bissalam.”
Ma’anar addu’ar ita ce “Allah ka kara wa wannan Dakin daukaka da girma da kwarjini, Allah duk wanda ya girmama shi, ya daraja shi a tsakanin wanda ya hajja ce shi ko ya yi umura, shi ma ka kara ma sa daukaka da girma da buwaya da tsoronka da bin ka. Allah kai ne aminci, daga wajenka aminci yake zuwa, mun gaida Ubangijinmu tare da sallama.”
Daga nan sai mutum ya nufi Hajrul As’wad ya sumbance shi da bakinsa, idan bai samu iko ba ya shafa da hannu sai ya sumbanci hannun, idan ma wannan bai yiwu ba, to ko daga nesa yake ya nuna wurin dutsen da niyyar ya taba sai ya sumbance shi da hannu. Akwai alamar da aka sanya na tiles wanda aka ja layi da shi tun daga Hajral As’wad din har zuwa bango har cikin gine-ginen saitin wurin, a nan mutum zai tsaya ya yi sumbar idan bai samu isa kaiwa ga dutsen ba. Daga nan sai ya fara dawafi.
Hajral As’wad yana da girman daraja a Musulunci, Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya sumbance shi zai yi ma sa shaida a ranar Tashin Kiyama.” Sannan ya zo a Hadisi cewa dutsen hannun daman Ubangiji ne (yadda ya dace da shi).” Ire-iren wadannan Hadisin ba a iya gane hakikanin ma’anarsu sai dai a karbe su a matsayin ibada.
Idan an shiga Ka’aba ba a yin nafilar gaisuwar Masallaci, Dawafin da Alhaji ko mai Umura zai yi shi ne yake makwafin nafilar, amma ga wanda ba Hajji ko Umura yake yi ba, shi zai iya yin nafilar. Idan kuma mai yin Aikin Hajji ko Umura ya shigo ya ga an tada sallar farilla, sai ya bi, ba zai ce sai ya kammala Dawafi ba. Koda mutum yana cikin Dawafin ne aka tsaida sallar farilla, zai yanke Dawafin ya tsaya daidai inda yake ya kabbara sallah. Ana yin sallama sai ya ci gaba da yin Dawafin.
Kamar yadda muka yi bayani a baya, ana fara Dawafi ne daga Hajrul As’wad bayan an sumbance shi ko an shafe shi ko daga hannu. Mutum zai sanya Ka’aba a hagunsa sai ya ce “Bismillah wallahu akbar, Allahumma imanan bika wa tasdiykan bikitabika wa wafaa’an bi ahdika wattiba’an lisunati Nabiyyika.”
Ma’anar addu’ar ita ce “Ina farawa da sunan Allah, Allah kai ne maigirma, zan yi Dawafin nan ne don imani da kai da gaskata littafinka da cika alkawarinka da bin sunnar Annabinka (SAW)”.
Haka mutum zai je ya kewayo, sai ya rika kirgawa duk lokacin da ya zo kan layin nan da ya fara Dawafin daga kansa har ya yi guda bakwai. Idan namiji ne, ana so ya yi sassarfa a kewaye na ukun farko, sauran kuma ya yi tafiya Idan kuma an cika da yawa ta yadda mutum ba zai iya yin sassarfar ba sai ya yi tafiya kawai, babu komai. Amma mata ba su yin sassarfa, duka nasu tafiya ce.
Ka’aba tana da kusurwowi guda biyu, Kusurwar Hajrul As’wad da ake farawa da ita, sai kuma wasu guda biyu da aka yi musu shinge su biyu ta yadda mutum ma ba zai iya tabawa ba (Tarihi ya nuna cewa wadannan kusurwowin biyu, nan ne lokacin da Kuraishawa suke gina Ka’aba da kudinsu na halas ya kare sai suka datse ginin), su wadannan ba a taba su ko an zo wucewa ta wurinsu. Amma idan mutum ya kewayo kafin ya zo Hajrul As’wad akwai Kusurwar Rukunil Yamani wanda shi ma ana shafarsa idan an samu hali, idan babu hali sai a nuna shi da hannun dama. Za a rika yin haka a duk kewayen Dawafin da za a yi.
Ana so a yawaita Zikirin Allah da addu’o’in da mutum ya zaba ya yi, don Malamai sun ce babu wata addu’a da aka ce dole ita za a yi. Sai dai wanda Hadisi ya kawo na Hajral As’wad. Addu’o’in da ake rubutawa a littafan nan da ake karantawa na Aikin Hajji masu kyau ne amma ba wai dole sai su ba. Idan mutum yana Dawafi sai ya yawaita fadin Subhanallah wal-hamdulillah wa la’ilaha illallah wallahu akbar wa laahaula wa laa kuwwata illa billahil aliyyil aziym, kamar yadda Ibn Majah ya ruwaito.
A wurin Rukunil Yamani kuma, Abu Dawuda da Imamus Shafi’i sun ruwaito Hadisi daga Annabi (SAW) ya ce idan aka zo nan za a iya karanta “Rabbana atina fid dunya hasanatan wa fil-akhirati hasanatan wa kina azaban nar”. Akwai Mala’iku a wurin da za su amsa wa mutum da amin. Za a iya yin wannan addu’ar a lokacin gudanar da Dawafin baki daya.
Zuwa mako mai zuwa za mu ci gaba da wani darasin cikin yardar Allah, inda za mu kawo muku darasi a kan yadda Manzon Allah (SAW) ya yi Aikin Hajji. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil aziym.