Shugabannin arewacin Nijeriya, ciki har da gwamnoni da Sarakunan gargajiya, sun gudanar da taro a Jihar Kaduna yau Litinin domin tattaunawa kan matsalar rashin wutar lantarki da sauran muhimman batutuwan yankin.
Wasu jihohi sun kwashe sama da mako guda ba tare da wutar lantarki ba, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin mawuyacin hali da tsananta matsalolin kasuwanci.
An shirya taron ne ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa, inda gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya shugabanci taron. Ya bayyana cewa matsalar lalata kayan aikin wutar lantarki ita ce silar katsewar, yana mai ba da shawarar saka hannun jari a sabbin layukan wutar lantarki da kuma amfani da wasu hanyoyin samar da makamashi domin rage aukuwar irin wannan matsala.
Gwamna Yahaya ya yi kira ga shugabannin yankin su tashi tsaye don samun mafita mai ɗorewa maimakon kawai yin maganganu ba tare da ɗaukar mataki ba.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya nuna muhimmancin samun haɗin kai domin fuskantar ƙalubalen tsaro da yankin ke ciki. A nasa bangaren, Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, wanda ya wakilci Sarakunan gargajiya, ya jaddada buƙatar tattaunawa kan asalin dalilan tsaro, da suka hada da talauci da rashin aikin yi.
Ya yi kira ga shugabannin su ɗauki matakan gaggawa domin samar da ingantacciyar makoma ga yankin.