Shi zaman aure zama ne da ya kunshi gaskiya, rikon amana da kuma tausayin juna. A wannan zaman ma’aurata ya kamata su sani akwai kyautatawa da girmama juna.
Uwargida ya kamata ta sani cewa a zaman aure fahimtar juna ita ce babban rabo, sannan girmama miji sai kuma hakuri, to a nan ya kamata a ce uwargida ta sani cewa miji shi ne sama da ita kuma a kasan sa take saboda haka dole akwai abubuwa da ya kamata ta sani cewar ya kamata ta kiyaye domin neman zaman lafia.
- Xi Jinping Ya Jaddada Muhimmancin Samar Da Kyakkyawar Fahimtar Al’ummantaka Ga Jama’ar Kasar Sin
- Yadda Ake Sultan Chips
 Wani lokaci za ka ga mace ba ta san yadda ake iya zaman hira da miji ba daga sun zauna inuwa daya to fa sai dai su fara fada, rashin iya hira da miji hakan na sa mace ta fita daga ra maigida, ko kadan zai daina jinta a ransa.
 Rashin Iya tambayar miji ya kamata uwargida ta sani cewa mata da dama suna fuskantar wanann matsalar da yawa mata ba sa sanin yadda za su tambayi miji zuwa unguwa ba ko kuma wani abu da ya shafi zamantakewarsu. Sai dai ka ga wata ta aiki yara su je su tambaya mata za ta fita.
Rashin iya sarrafa kalamai
Uwargida kar ki kasance mai sake ki yi magana da miji babu taunawa babu lankwasa harshe, tabbbas yin haka na sawa mace ta fice daga ran maigida.
Rashin tattalin dukiyar maigida
Hakan na taimakawa sosai wajen rage taurarin uwargida a zuciyan maigida, ke kenan duk abin da miji ya ajiye babu ruwanki ba za ki taba ba sai ido akai hakan na sanya miji ya gaji da mace.
 Saboda haka uwargida yana da kyau ki kiyaye duk wadanan abubuwa domin samun rayuwa mai dorewa a gidan miji.
 Kazanta ,uwargida yana da kyau ta kiyaye wannan hali, kar ki kasance mai rashin kula da tsafta. Allah ya bamu ikon kiyayewa amin.