A makon da ya gabata ne ‘yan bindiga suka sako daliban makarantar Kuriga 137 da ke Jihar Kaduna wanda suka yi garkuwa da su a makonni baya.
Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani, ya bayyana cewa dalibai 137 ake yi garkuwa da su ba a ranar 7 ga Maris, 2024, a kauyen Kuriga da ke cikin karamar hukumar Chikun a jihar, ba dalibai 287 da ake ta yayatawa a kafafen yada labarai.
- Tsananin Zafin Rana Na Janyo Mana Cutar Daji – Shugaban Zabaya Na Kaduna
- Gwamnan Zamfara Ya Yi Kira A Kara Yawan Sojoji A Jihar Don Yaki Da ‘Yan Bindiga
Gwamnan ya bayyana adadin daliban ne a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin Channels a shirin siyasa. Ya ce sojoji tare da hadin gwiwar jami’an tsaron sa-kai na Jihar Zamfara sun sami nasarar kubutar da dukkan daliban daga hannun ‘yan bindiga daga wuraren da suke rike da su.
Makonni hudu da suka wuce ne dai aka sace daliban daga makarantar firamare da sakandare ta Kuriga.
Shalkwatar tsaro ta bayyana cewa adadin dalibai guda 137 ne, ba kamar rahoton da ake bayyana na cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 287.
Sai dai kuma gwamnan ya yi takaicin mutuwar malamin makarantar a hannun masu garkuwan. Ya mika ta’aziyarsa ga iyalan da ‘yan’uwan malamin, sannan ya yi alkawarin mika daliban ga ‘ya’yansu.
Ya ce, “Mutum daya ne ya rasa ransa a hannun masu garkuwan shi ne malamin da suka tafi da shi, amma dukkan daliban guda 137 an samu nasarar ceto su cikin koshin lafiya. Muna takaicin abun da ya faru da malamin wanda jami’an tsaro su-ka bayyana mana cewa ba shi da lafiya, amma dukkan daliban an kubutar da su kuma suna hannunmu.”
Haka kuma gwamnan ya bayyana cewa Sheikh Ahmad Gumi bai da hannu wajen ceto daliban, shehin malamin bai tattauna da ‘yan bindiga ba kafin sako daliban.
sai dai kuma masana na ganin cewa akwai tambayoyin da aka kasa amsawa wajen ceto daliban, kamar nawa aka biya ko kuma ba a bayar da kosisi ba? wani irin dubara aka bi wajen samun wannan nasara? Salun-alun ‘yan bindigan suka saki daliban ko sai da aka yi musayar wuta?
duk wadannan wasu tambayoyi ne wanda aka kasa amsawa game da ceto daliban Kuriga guda 137.