Mutane da dama idan sun tashi sayan kwamfuta sukan yi la’akari da kyalkyalin kwamfuta ko sunan kamfanin da ya kera kwamfuta din.
Duk da cewa sunan kamfani yana da matukar tasiri musmman kamfanin da ya yi suna wajen samar da ingantattun na’urori. To amma wasu lokutan a kan yi zaben tumun dare, sai ka ga mutum kwana biyu da sayan kwamfuta, amma ba ta masa abin da yake so, tuni sai ya fito yana neman sayar da ita, domin ya sayi wadda ba ta dace da bukatar sa ba. Kuma dole ne ya yi asara wajen sake sayar da ita.
Idan mutum ba shi da ilimin fahimtar ingancin na’urori, to yana da kyau ya tuntubi wadanda suka sani musamman dalibai masu nazari a fannin ilimin kwamfuta.
A matakin farko yana da kyau mutum ya tantance bukatar irin kwamfutar da ta dace ya saya, ta girke (Desktop) ko ta yawo (Laptop). Na biyu kuma karfin aljihu (adadin kudin kwamfutar), na uku kuma ga su kamar haka;
-Masarrafi (Processor): shi ne a matsayin kwakwalwar na’urar kwamfuta, kuma ana bayyana saurinsa wajen sarrafa aiki a matakin GigaHertz (GHz). Yana da kyau a sayi kwamfuta wadda take mafi saurin sarrafa aiki, amma kuma irin wadannan sukan yi tsada sosai saboda saurinta shi ne darajarta.
Shi ya sa a wannan matakin yake da kyau mutum ya yi nazari a kan bukatarsa ta mallakar kwamfuta da kuma irin aikin da zai yi da ita. Idan ya kasance aikin da zai yi da ita bai wuce rubuce-rubucen ba, irin na aikin ofis ko makamancin haka, ba ya bukatar sayan kwamfuta sama da 1Ghz na masarrafi.
Idan kuma ya kasance aikin sa mai nauyi ne kamar aikin sarrafa Hotuna, Bidiyo masu nauyi da inganci sosai, to a nan akwai bukatar babban masarrafi kamar 1.5Ghz zuwa 2.5Ghz ko 3.0Ghz.
-Rumbun Aiki (RAM ko Memory): Kusan duk saurin masarrafi (CPU) a kwamfuta ya dogara ne da girman rumbun aiki. Dukkan aiyukan da ake yi da na’urar Kwamfuta a cikin wannan rumbu ake gudanar da shi. Kuma ana auna adadin girmansa a tsarin ma’auni na Gigabyte (GB). Saboda haka a kowacce irin bukata ana so ya kasance mai girma akalla 4Gigabyte.
-Rumbun Ajiya (Hard Disk Dribe): Wannan shi ne wajen da ake adana dukkan aiyuka, manhajojin aiki, manhajar sarrafa na’ura ma a cikinsa ta ke da sauran abubuwan da ake iya adanawa a kwamfuta. Shi ma girmansa yana taka muhimmiyar rawa wajen sayan kwamfuta.
A shekarar 2014 aka samar da sabon samfurin rumbun ajiya na musamman mai suna ‘solid state’. Ya bambanta da na asali kamar haka; Saurin aiki da kuma kasancewarsa babu tarkace masu motsi a cikinsa kamar na asali. Amma kuma yanada matukar tsada sosai. A nan mutum zai iya sayan kamar 320GB, 500GB, 650GB, 750GB ko 1Terrabyte.
-Injin Sarrafa Hoto (Graphics Card): Wannan ma yana da matukar fa’ida, saboda shi ne jigo wajan sarrafawa da tace hoto da bidiyo a kwamfuta domin bada ingantaccen hoto a manunar kwamfuta (Display). Haka kuma akwai manhajoji wadanda aikinsu ya dogara ga ingancin hoto ko bidiyo domin samun cikakken sakamakon aikin su Misali HD Bideos da Adbance Games. An fi samun na musamman masu inganci fiye da wadanda suka zo a cikin kwamfuta. Sai dai tsada sosai kuma an hada su da kwamfuta ta hanyar USB ko kuma Hanyar karawa kwamfuta sassa na musamman (edpansion slot).
-Manhajar sarrafawa (Operating System): Kusan kaso tamanin (80%) na kwamfutoci da ake aiki dasu a duniya suna amfani da manhajar sarrafa kwamfuta na kamfanin Microsoft, wato Windows. Wasu lokutan a kan sayar da kwamfuta da windows a kanta, haka zalika wasu akan sayar da su babu windows akansu. Sai dai mutum ya zabi irin window din da yake so domin a saka masa ko ya saka da kansa. A halin yanzu windows mafi dacewa a kan kwamfuta shi ne windows 10 ko kuma windows 8.1.
Wadannan abubuwa sune suka fi dacewa da ayi la’akari da su a duk lokacin da aka tashi sayan kwamfuta.