“Za a cire tallafin man fetir, sannan akwai hasashen tashin gwauron zabo na farashin kaya tare da bukatar neman karin albashin ma’aikatan gwamnati daga shugabannin kungiyoyi wadanda sun san gaskiyar abin da ke faruwa, amma sai su yi kamar ba su sani ba. Har ila yau, wajen magance matsalar bambancin farashin Dala tsakanin na gwamnati da kuma kasuwar bayan fage, ana kyautata zaton wannan sabuwar gwamnati za ta sake yi wa farashin Dala kwaskwarima, inda farashin gwamnati zai kasance daga Naira 430-450 zuwa 550 a tashin farko”.
–Abin Da Kuka Yi Tsammani A 2023, Da ranar 29 Ga Disamba, 2022.
Wannan shi ne hasashena na hudu da na yi tun daga shekarar 2019. Baya ga wasu al’amura da suka faru, inda na tsinci kaina a wani yanayi maras dadi kamar lokacin annobar Korona da kuma abin mamakin da ya faru da Afirka a karshen wasan cin kwallon kafa ta duniya, maimakon Kasar Senegal ko Aljeriya sai ga Moroko a kan gaba, wannan ya sani sake kiyayewa yadda ya kamata.
A wannan shekara, zan fara ne da wasannin kwallon kafa. Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a halin yanzu na cike da farin ciki tare da kwarin guiwa, amma me ya sa? Koda-yake dai wajibi ne su kara kaimi wajen yin kwazo, musamman ganin yadda suka kwashe shekaru ashiri ba tare da samun nasarar cin kofi ba.
Komai yana tafiya yadda ya kamata, domin kuwa kungiyar kwallon kafar na da kyakkyawan shiri tare da tsari, musamman idan aka yi la’akari da ‘yan wasansu masu kula da tsaron baya da kuma tsakiya dukkanninsu suna yin matukar kokari.
Har ila yau, labarin ba zai canza a wannan shekara ta 2024 ba. Ina fatan abin da ya faru da zukatan miliyoyin magoya baya shekaru ashirin da suka gabata, ba zai sake faruwa a nan gaba ba. Duk dai da cewa, yiwuwar kai bante ba a kan kungiyar kwallon kafar Arsenal din yake ba. Kungiyar na da matukar karfi, amma duk da haka tana samun rashin nasara a wasu lokutan.
Na fara da wasannin kwallon ne sakamakon ganin cewa, 2024 ba shekara ce ta hayaniyar siyasa a Nijeriya ba kamar yadda aka saba. A 2023, mun yi siyasar shekara hudu a cikin shekara guda. Baya ga wasu manyan Alkalai wadanda suke samun kudin shekara hudu a shekara guda kacal, inda wasu mashahuran ‘yan siyasar kuma ke karar da abin hannunsu tare da rabukewa guri guda. Saboda haka, ya zama wajibi a wannan shekara ta 2024 su fito ko ta halin kaka, domin ganin sun samu sun murmure don fita daga kangin da suke ciki, idan kuwa ba haka ko shakka babu za su yi asarar magoya bayansu baki-daya.
Kafin watan Yuli, wasu daga cikin manyan ‘yan siyasa wadanda suka iya riskar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu tare da neman alfarma a wurinsa, wadannan makomarsu na hannunsu; domin kuwa za su ci gaba da bayyana manufarsu da kuma rashin kunyarsu a fili. Kazalika zuwa karshen shekara kuma, alfarmar da shugaban kasar ke yi za ta tsaya cak, haka nan su ma ‘yan adawar sai kuma a shiga dimuwa.
Ko shakka babu Jihar Ido, Ondo da kuma Kano, Hukumar INEC ta kasa na shirye-shiryen sake wasu zabubbuka na ‘yan majalisar dattijai da na majalisar wakilai 11 da kuma majalisar jihohi 22. Fatan da nake yi ya kasance ba a samu abubuwan mamaki ba. Idan wani abu ya faru, ya kasance babbar jam’iyya mai mulki ta kasa (APC) ta karbe kujerun Sanatoci biyu ko uku, za ta kara samun karfi a majalisa, haka nan zai kasance a majalisar jihohi su ma.
A watan Satumba da Nuwamba, za a gudanar da zabubbuka a jihohi guda biyu, Jihar Edo da kuma Ondo.
Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, wanda ya fara zangon mulkinsa a matsayin gwamnan APC, inda daga bisani ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a zangonsa na biyu, yana yunkurin mika kujerar gwamnan ga wanda yake son ya gaje shi a jam’iyyar tasa ta PDP. Koda-yake dai, zabe ne kadai zai raba gaddama.
Har wa yau, a cikin jerin wadanda ke kan gaba wajen adawar siyasa a halin yanzu, Obaseki na kan gaba wajen fafatawa da tsohon mai gidansa Adams Oshiomhole, wanda a halin yanzu ke jam’iyyar APC a matsayin Sanata; sai kuma mai gidansa a halin yanzu, Nyesom Wike; guda daga cikin ministoci, wanda shi ba PDP ba, ba kuma dan jam’iyyar APC ba; da mataimakinsa Philip Shauib, wanda suka yi faman fafatawa tare da samun sabani har karshen zangon mulkin nasu.
Obaseki yana lissafa abubuwa da dama, daga cikinsu akwai batun son ya taimaka masa ya kai ga mika wa wanda yake so ya gaje shi a kujerarsa ta gwamna, tsohon Shugaban Bankin Sterlin, Asue Ighodalo.
Hasashena a nan, duk da kulle-kulle da tuggun irin na Obaseki, dan takararsa ba zai kai bantensa a zaben watan Satumba ba. abubuwan da ya shuka tsawon shekaru takwas, ko shakka babu su zai girba ko ya gani a kwaryar shansa a siyasance.
Babbar matsalar samun nasarar APC a wannan jiha, Adam Oshiomhole, sakamakon karkatar da dukkanin mukaman gwamnatin tarayya da aka yi zuwa Arewacin Jihar Edon, kawai don a bakanta wa wasu, bangaren kudanci kuma wadanda su ne matattarar zaben, akwai yiwuwar su fi karkata a kan jam’iyyar LP, wanda dan takarar ya fito daga yankinsu. Sai dai idan kuma dan takarar da APC ta tsayar ya zama mai matukar nagarta, hakan zai iya bayar da matukar mamaki.
A gefe guda kuma Jihar Ondo daban ce. Bayan tsawon watanni da aka shafe ana fafatawa da marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu, inda a karshe Aiyedatiwa ya samu nasarar zama gwamnan rikon kwarya, yanzu kuma ya zama gwamna mai cikakken iko, yadda alamu suke nunawa zai iya faduwa zabe sakamakon kalubalen da ke waje da kuma ita kanta jam’iyyarsa.
Ya yi yakin neman zabensa da ya kamata ya yi nan gaba, amma yakin da ke tsakanin wannan lokaci zuwa watan Nuwamba, na tabbatar da cewa; ko shakka babu zai iya yin awon gaba da shi daga magoya bayan Akeredolu da kuma wasu daban, ciki har da Sanata Jimoh Ibrahim.
Abin da ya shafi Jihar Kano kuma, kotun koli ta bayyana daga nan har har zuwa 15 ga watan Janairu kafin ta kai ga yanke hukuncin. Har ila yau, tarihi ba zai taba manta wa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ba, kamar yadda na fada a rubutun da na yi a baya, cikin shekara 20 da suka gabata; shari’u ‘yan kadan ne inda kotunan kasa suka yi hukunci iri guda kotun koli ta canza.
Shugaban Kasa Tinubu, ya yi matukar tayar da kura ta watanni bakwai da suka gabata, haka nan a wannan sabuwar shekara dole ya kara jajircewa tare da sanya idanu, musamman a kan abokanan aikinsa (ministoci), ta hanyar sauya wadanda bas u yi wani abin a zo a gani ba, yayin da yake cika shekara daya a kan karagar mulki.
Sannan, babban kalubalen da zai ci gaba da fuskanta shi ne batun tattalin arziki, musamman ganin yadda hauhawar farashi ya karu da kashi 27.3, darajar naira ta fadi da kashi 50 cikin 100 cikin wata shida, rashin aikin yi ke ci gaba da ta’azzara, don haka duk abin da aka samu a 2024 ba zai isa ba, sai an samu gibi.
Yanzu haka, naira ta kasa tsayuwa da kafafunta, tana daf da kullewa a kan 1500 kowace dala a kasuwar bayan fage, don haka sai dai idan an yi matukar sa’a man fetir da gas sun matukar tashi, sannan za a samu saukin al’amuran.
Abu na biyu kuma shi ne batun noma ta yadda za a samu farashin kayan abinci ya sauko daga kashi 32 da yake a halin yanzu, ta hanyar samun damuna mai albarka tare kuma da samun wadataccen tsaro a fadin kasa baki-daya, su ne za su taimaka wajen bunkasar samun abinci.
Bugu da kari, babbar matsalar da Babban Bankin Nijeriya ya ke da shi, idan aka ajiye batun alkawarin da ya yi na kokarin daidaita farashi a 2024, rahoton da mai gudanar da bincike ya gabatar ya shafe komai da komai.
Haka zalika, ka da a yi tsammanin samun wadatacciyar wutar lantarki saboda dalili guda: ko da gurare hudu da ke samar wa da Nijeriya wutar lantarki za su iya sama mata sama da mega wat dubu 2 kowannensu, wanda hakan ma ba zai taba yiwuwa ba, ba a taba samun wadatacciyar wuta ba.
Haka nan, batun samar da gas, batu na gaskiya shi ne babu gas din. Sannan, kamfanin gas din na Nijeriya bashi ya yi masa katutu, har ila yau, yanayin kasuwa kuma ya dakile ‘yan kasuwa masu zaman kansu.
Haka nan, duk wanda ke tsamnin za a samu sauki a harkar shigo da man fetir ko samun saukin farashi, wani abu ne wanda za a jima ana jira. Sannan, batun gyara matatun man fetir, shi ma abu ne da sai ya dauki lokaci, matatar mai ta Dangote kuma ba ta iya bayar da wadataccen man da ke bukata ba, sai bayan wani lokaci.