Kwanan baya, wani jirgin ruwan dankon hajoji dauke da motoci masu aiki da sabbin makamashi da yawansu ya kai kimanin 5000, ya tashi daga tashar jirgin ruwa ta Taicang dake birnin Suzhou, ya nufi tashar jirgin ruwa ta Zeebrugge dake kasar Belgium, don biyan bukatun dake habaka a wurin.
Kamfanin BYD mai jarin kasar Sin dake mallakar wannan jirgi, ya sayar da irin wadannan motoci har dubu 417.2 ga ketare a shekarar bara, wanda ya kai matsayin farko a duniya a wannan bangare. Idan mun yi hangen nesa, akwai fatan rage fitar da hayaki mai dumama yanayi ta irin wannan mataki, da kuma taimakawa fitar da karin kayayyaki masu kare muhalli zuwa ketare, don gaggauta bunkasuwar sha’anin amfani da sabbin makamashi a wurare daban-daban.
- Xi Ya Zanta Da Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Ta Tarho
- Sin Na Bukatar Ma’aikatan Masana’antu Masu Kaifin Basira Fiye Da Miliyan 31 Zuwa 2035
Fitar da motoci masu aiki da sabbin makamashi, ya wuce batun samarwa duniya ingantattun hajoji, inda har ma ya kai muhimmin karfi na fadada cinikin shige da fice. Gwamnatin Sin ta gabatar da alkaluma a jiya cewa, a shekarar 2024 da ta gabata, yawan kudin cinikin waje da aka yi a kasar Sin ya kai kimanin dala triliyan 6, wanda ya karu da kashi 5%, kan na makamancin lokaci na shekarar 2023, matakin da ya kai sabon matsayi a tarihi.
Cimma wannan matsayi ba abu ne mai sauki ga kasar Sin ba, duba da cewa, ana ta kara nuna karfin aiwatar da manufofin ba da kariyar ciniki, da barkewar rikice-rikice a wasu wurare a duniya, matakin da ya bayyana kuzari da karfin bunkasar tattalin arzikin Sin.
To ko mene ne ma’ana wannan rahoto ga duniya? Ba ma kawai Sin ta gabatar da karin sabbin ingantattun kayayyaki masu kare muhalli a wannan bangare ba ne, har ma ta habaka kasuwarta, da samar da yanayi mai kyau na samun bunkasuwa.
Hukumar WTO ta ba da alkaluma dake nuna cewa, saurin shigo da kayayyaki zuwa Sin ya zarce na duniya da kashi 1%, daga watan Jarairu zuwa Satumban bara, inda aka yi kiyasin cewa, kasar Sin za ta ci gaba da zama a matsayi na biyu a duniya wajen shigo da kayayyaki daga ketare. Kazalika, manazarta na bayyana cewa, Sin na da karfin habaka bukatunta na shigo da kayayyaki, duba da yadda take habaka bukatunta na cikin gida, yayin da yawan kudin da Sin din za ta kashe wajen shigo da kayayyaki daga kasashe masu tasowa kawai zai kai fiye da dala triliya 1, abin da ya alamanta cewa, kasuwar Sin za ta zama wata babbar kasuwa ga dukkanin fadin duniya. (Amina Xu)