Shan ko wane ruwa daga cikin wadannan yana saukarwa da mace ni’ima mai kyau irin wacce maza su ke so, kuma ko wanne ruwa akwai yadda ake sarrafa shi da mahadan da za su saukar da wadatacciyar ni’ima.
Ga kadan daga cikin yadda ake sarrafa wasu ruwan daga ciki:
- Kamfanonin Taki Na Gida Za Su Iya Taimaka Wa Gwamnati Wajen Tallafa Wa Manoma
- Hukumar Kula Da Ayyukan Duba-gari Ta Kasa Za Ta Karrama Shugaba Tinubu
1) Ruwan Kankana, Ayaba Manya Uku, Kankana Kwata Da Tuffa: Ki hada ki markada ki zuba madarar ruwa gwangwani daya, zuma yadda kike so, ki sa kankara ya yi sanyi, ki sha kamar lemo yana da kyau sosai.
2) Ruwan Tumatir: Ki markada tumatir biyu, ki zuba ruwan a cikin kwai uku, ki sa magi da albasa ki soya ya yi ruwa-ruwa ki ci. Shi ma ya na saukar da ni’ima sosai da sosai
3) Ruwan kwakwa: ki fasa kwakwarki ki tsiyaye ruwan cikin kwakwar, sannan ki bare bakin bayan kwakwar ki goga kwakwar da ‘greater’, sannan ki markada a ‘blander’, sai ki zuba ruwa a kan markadaddiyar kwakwar ki tace ruwan ki fid da dusar. Da ma kin bare dabinonki cikin gwangwanin madarar ruwa daya. Ki jika dabinon ya yi laushi sai ki markada ya yi laushi sosai, sai ki zuba a kan ruwan kwakwar, sannan ki zuba ruwan da kika fasa kwakwar ya zubo a ciki. Ki zuba zuma da garin madara cokali uku a ciki, ki juya sosai. Ki sa a firij ya yi sanyi ko ki saka kankara. Idan ba ki son sanyi sai ki sha a haka. Ki yini kina sh, kar ki barshi ya kwana.
Za Mu Ci Gaba A Mako Mai Zuwa