A ranar Talata 18 ga watan Fabrairu ne Hukumar Kula da Ayyukan Duba-gari ta Kasa za ta gudanar da babban taronta na shekara-shekara inda ake sa ran za ta karrama wasu fitattun ‘yan Nijeriya ciki har da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnonin Nijeriya 6.
Shugaban hukumar, Dakta Yakubu Baba Mohammed ne ya bayyana haka a yayin ziyarar da ya kai a Hedikwatar kamfanin buga jaridar LEADERSHIP da ke Abuja ranar Litinin.
- Shugaba Xi Ya Halarci Taron Kamfanoni Masu Zaman Kansu Tare Da Gabatar Da Jawabi
- Kotu Ta Hana Gwamnatin Tarayya Riƙe Wa Kano Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi
Ya ce, an kafa hukumar ce a shekarar 1902 a matsayin jami’ai masu Duba Gari wanda aikin su ya yi makukar tasiri wajen tabbatar da tsaftace muhalli da samar da kariyar cuttuka a tsakanin al’umma a wanccan lokacin.
Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu ayyukan hukumar bai tsaya a kan kula da tsaftace muhalli da abinci kadai ba, suna kula da tasirin sauyin yanayi da kuma fadakar da al’umma yadda za su amfana da trallafin sauyin yanayin da ake samu daga Majalisar Dinkin Duniya.
A nasa jawabin, Babban Manajan Daraktan kamfanin, Alhaji Mu’azu Elezah ya nuna bukatar hukumar ta kara kaimi wajen yayata wa al’umma ayyukanta domin zuwa yanzu mutane kadan ne suka san kasancewar hukumar da ayyukanta a sassan kasar nan, “Ya kamata ku zuba jari sosai wajen fadakar da al’umma irin ayyukanku, da kuma yadda mutane za su amfana daga tallafin yaki da sauyin yanayi na majalisar dinkin dunuya” in ji shi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp