Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zaici gaba da kawo muku abubuwan da mata za su sha domin karin ni’ima:
- Kasar Philippines Za Ta Dandana Kudarta Game Da Gudummawar Soja Da Amurka Ta Ba Ta
- Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji Kan Kayayyakinta
4) Ruwan Zogale: Amfanin ruwan zogale ba zai lissafu ba a maganin cututtukan da ya ke yi ma na a jikinmu. Amma zan yi bayanin amfaninsa a bangaren karin ni’ima a jikkunanmu ne kawai.
A- ki tsinke zogale ki wanke ki tafasa sosai ki tace ruwan zogalen ki zuba kaninfari da citta ki tafasa. Sai ki sauke ki dinga kurba da zafinsa kamar shayi. Ya na gyara jiki ya saukar da ni’ima sosai. Ya na karawa mace kuzari a jikinta sosai, sannan ya na karawa mace juriya.
B- Ki tsinke zogale ki wanke ki markada ganyen a ‘blander’ ko ki mutstsika da hannunki ki kara ruwa a kai ki tace ki matse dusar. Ki zuba madarar ruwa gwangwani daya a cikin ruwan zogale cikin jug daya. Ki sa zuma ta ji sosai. Ki juya ya hadu ki dinga sha. Gaskiya ba shi da dadin sha, sai dai akwai shi da aiki; ni’ima lutsutsu! Domin duk bushewar da mace tayi da rashin ni’imarta sai ni’ima ta zo.
C- A nan ganyen zogalen da kika tafasa sai ki zuba a faranti ki yanka tumatir manya guda uku, ki yanka gurji (cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri kadan, mai kadan. Kar ki sa wulikuli. Zai yi miki maganin basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano sosai.
5) Ruwan Dabino: Ki bare dabinonki rabin kwano, ki jika da ruwa. Idan ya yi luguf sai ki markada a ‘blander’. Za ki gan shi da kauri kirtif. Sai ki ajiye a firinji; duk sanda za ki sha sai ki debi cokali biyu ki zuba a kofi, ki juye madarar ruwa gwangwani daya, ki sa garin minannas karamin cokali ki juya sosai. Idan ya yi kauri da yawa ki kara ruwa kadan ki kuma juyawa, ki shanye duka. Bayan awa uku da shanki za ki tsinci kanki cikin wani yanayi na lutsutsu.
6) Ruwan Rake: Ki bare rake ki yanka gutsu-gutsu ki daka a turmi ko ki markada a ‘blander’ ki na yi ki na kara ruwa a dusar raken ki na matsewa. Idan kin sami ruwan rake kamar cikin jog daya.
Sai ki sami ruwan tafasashshen baure jog daya.
Sai ruwan jangari da jangagai da alewar mata da a ka tafasa su guri guda a ka tace su ma jog zaya.
Sai ki zuba wannan ruwayen naki a wuta ki zuba zuma kofi daya, ki yi ta dafawa har sai ruwan ya kone ya zama kamar cikin jug daya, sai ki sauke.
Amma za ki sa kaninfari da kayan kamshi a dahuwar. Idan ya huce sai ki juye a abu mai kyau. Ba zai lalalce ba.
Kullum ki sha ludayi daya. Zai ratsa jikinki ki sami dauwamammiyar ni’ima. Tsimin rake Kenan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp