Wani abin al’ajabi, mazauna garin Birnin Magaji ta jihar Zamfara sun yi awon gaba da wasu mata da ‘yan uwan ‘yan bindiga a wani mataki na ramuwar gayya kan sace-sacen da ‘yan ta’adda suka yi a yankin.
Wani shugaban matasan yankin ya shaida wa PRNigeria cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu mutane a lokacin da suke aikin gona.
- ‘Yan Bindiga Sun Karbe Ikon Kauyuka 400 A Zamfara -Masani
- ‘Yansanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga A Masallacin Juma’a A Zamfara
“’Yan bindigar dauke da muggan makamai sun yi wa gonakinsu kawanya tare da yi wa manoma barazana kafin su yi awon gaba da su.
“A ‘yan kwanakin nan, mutane da yawanmu a yankin bama iya zuwa gona, ko da mutum yana gida zuciyarsa cike take da barazanar tsoron za su zo su yi garkuwa da shi don neman kudin fansa,” inji shi.
PRNigeria ta rawaito cewa, a wani yana yi na ramuwar gayya, matasan yankin sun kama matan barayin mutanen ciki har da wata mace mai juna biyu da ke kan hanyarta ta komawa gida.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka ana ci gaba da tattaunawa tsakanin shugabannin yankin da ‘yan fashin domin ganin an shawo kan matsalar.
Duk da haka, ba a iya tabbatar da ko ‘yan sanda na da hannu a tattaunawar ba har zuwa lokacin hada wannan rahotan ba.