Kungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Nijeriya, wato Arewa Consultative Forum (ACF), ta yi magana da kakkausan harshe kan abin da ta kira yunkurin da ake ta yi na kawo cikas ga harkokin Matatar Man Dangote da Kamfanin Sinadarai na Petrochemicals da ke Ibeju-Lekki, Legas.
ACF ta nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin “makirci da aka boye” da ke nufin lalata mafi girman matatar man cikin gida mallakar ’yan Nijeriya.
- ‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar
- Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos
A cikin wata sanarwa da Sakatarenta na Yada Labarainta na Kasa, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, ya fitar, Arewa Consultatibe Forum (ACF) ta bayyana damuwa kan irin jerin matsalolin da suka rika hana ci gaban Matatar Man Dangote tun daga kafuwarta har zuwa matakin aikinta na yanzu.
A cewar kungiyar, wadannan kalubalen sun hada da takurawar dokoki daga hukumomin gwamnati, karancin isar da danyen mai daga Kamfanin Man Kasa na Nijeriya (NNPC), matsalolin da suka shafi farashin kayayyaki, da kuma tsoma bakin kungiyoyin ma’aikata da na dillalan man fetur.
ACF ta fi mayar da hankali ne kan rawar da Kungiyar ’Yan Kasuwar Man Fetur ta Nijeriya (IPMAN), Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (NUPENG), da Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (PENGASSAN) suka taka, tana zarginsu da shiga cikin ayyukan tada hankali, ciki har da zanga-zanga da barazana, wadanda suka kara dagula harkokin aiki na matatar man.
“Yanzu abin yana kara bayyana a fili cewa akwai wasu boyayyun kungiyoyi da ke da niyyar ganin wannan babbar masana’antar cikin gida ta gaza,” in ji sanarwar. “Wannan yana nuna irin tsarin makirci daya da ya sa matatun man gwamnati guda hudu na Nijeriya suka gaza aiki yadda ya kamata.”
ACF ta nuna goyon baya ga matakin da Kamfanin Dangote Group ya dauka na neman kariya ta shari’a domin tabbatar da ci gaban ayyukansa, tare da zargin kungiyar PENGASSAN da karya umarnin kotu da ke hana ta kawo cikas ga ayyukan matatar man.
Kungiyar ta bayyana wannan ketare iyaka a matsayin raini kai tsaye ga tsarin shari’a na Nijeriya da kuma misali mai hadari ga dangantakar masana’antu a kasar.
Kungiyar ta kuma nuna goyon baya ga ra’ayoyin da Sanata Adams Oshiomhole da Sanata Mohammed Ali Ndume suka bayyana kwanan nan, inda suka ba da shawarar cewa a bai wa matatar man damar ta daidaita harkokinta kafin a kawo batun kungiyoyin kwadago a cikinta.
A cewar ACF, “ba za ka iya sanya kungiyar kwadago a wurin aiki da har yanzu yana cikin matakin farko na fara aiki ba.”
Bugu da kari, ACF ta yi kira da a kafa kwamitin binciken shari’a domin gudanar da cikakken bincike kan yawan yajin aikin da ake ta yi wanda ke nufin manyan cibiyoyi na gwamnati da masu zaman kansu. Ta ce wannan mataki zai taimaka wajen gano mutanen da ke bayan abin da ta bayyana a matsayin shiryayyen kamfen na hana ci gaban masana’antu a Nijeriya.
Saboda haka, kungiyar ta shawarci kungiyoyin kwadago da su guji duk wani aiki da zai iya kawo cikas ga kokarin zuba jari na cikin gida.