Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa (ACG) ta sanar da cewa za ta ware kudi har dala biliyan 50, don taimakawa wajen samar da ababen more rayuwa a nahiyar Afirka.
Shugaban bankin ci gaban Musulunci, Dokta Muhammad Al Jasser ne ya sanar da hakan a taron tattalin arzikin kasashen Larabawa da Afirka da aka gudanar a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
- Dokar Fallasa Barayin Gwamnati Na Nan Daram – Gwamnatin Tarayya
- Xi Ya Amsa Wasikar Da Matias TarnopolskyTarnopolsky Ya Rubuta Masa
Kasashe da yawa a Afirka na fuskantar matsalar sauyin yanayi.
A cikin sanarwar hadin gwiwa, kungiyar ta ce: “Duba da alakar da ke tsakaninmu za mu samar da abubuwan ci gaba masu dorewa da kuma samar da kudade don inganta sauyin yanayi.
“Yarjejeniyar da kuma taimakawa wajen cike gibin zuba jari a fannin samar da makamashi, da suka hada da karancin makamashin ‘carbon’, daidaita sauyin yanayi da kuma samar da abinci.”
Bayar da tallafin ACG zai tallafa wa shirye-shirye a fannoni kamar tsaro na makamashi da canjin makamashi, hadin kai a nahiyar, harkokin kasuwanci, shirye-shiryen jinsi da matasa, samar da kudade da sauran ababen more rayuwa.
A cikin sanarwar ta ACG ta ce “Mun amince da bukatar magance wadannan kalubale ta hanyar daukar matakan da suka dace a kan lokaci.”
A madadin kungiyar ta ACG, Al Jasser ya ce: “Tabbas a shirya muke mu cika alkawarin da muka daukar wa Afirka.”
“Duk da haka, muna sane da kalubalen ci gaban da nahiyar ke fuskanta – illar da cutar COVID-19 ta haifar a duniya a baya-bayan nan, da kalubalen samar da abinci, da kuma kara tabarbarewar tattalin arziki.
“Mun himmatu wajen yin aiki kafada da kafada da kasashen Afirka da kungiyoyin jama’a, da kamfanoni masu zaman kansu, da sauran cibiyoyin raya kasa.”
Kungiyar ta kasance mai goyon bayan kasashen Afirka da dama kuma ta zuba jarin sama da dalar Amurka biliyan 220 a yankin zuwa yanzu.
Sanarwar ta kara da cewa, “Mun sake jaddada aniyarmu na tallafa wa ci gaban kasashen Afirka.”
Mambobin kungiyar sun hada da Asusun Raya Abu Dhabi, Bankin Larabawa don Ci gaban Tattalin Arziki a Afirka, Asusun Larabawa don Ci Gaban Tattalin Arziki da Ci Gaban Al’umma, Shirin Raya Gabas na Larabawa, Asusun Lamuni na Larabawa, Bankin Raya Islama, Asusun Kuwait. Bunkasa Tattalin Arziki, Asusun OPEC na Ci Gaban Ƙasashen Duniya, Asusun Raya Kasar Qatar da Asusun Raya Kasar Saudiyya.