Dandalin biyan kudade na NetsUnion dake kasar Sin, da babban dandalin biyan kudaden sayayya ta intanet na kasar UnionPay, sun sanar da karuwar biyan kudade tsakanin masu sayayya ta kafofin intanet, yayin hutun bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da bikin tsakiyar kaka da suka kammala.
Hakan na kunshe ne cikin alkaluman da babban bankin kasar ta Sin ya fitar a Alhamis din nan. Babban bankin ya kara da cewa, yayin hutun na kwanaki takwas da aka kammala a jiya Laraba, adadin biyan kudade ta dandalolin biyu ya kai yuan tiriliyan 13.26, kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.86, inda adadin ya karu da yuan tiriliyan 1.86 kan na makamancin lokacin hutun na shekarar bara.
Kazalika, dandalolin biyu sun gudanar da hada-hadar biyan kudade kusan biliyan 41.6 a lokacin na hutu, wanda hakan ke wakiltar karuwar hada-hada biliyan 9.5, kan ta lokacin hutun bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin na shekarar bara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)