A yau Talata, bayanai a hukumance sun nuna cewa, adadin kudin ajiyar Sin na ketare ya kai dalar Amurka tiriliyan 3.2024 ya zuwa karshen watan Disamban shekarar 2024, wanda ya ragu da dala biliyan 63.5, ko kashi 1.94 bisa dari, idan aka kwatanta da karshen watan Nuwamban bara.
Tattalin arzikin kasar Sin ya gudana yadda ya kamata, ya kuma samu ci gaba mai dorewa, tare da samun ci gaba wajen bunkasuwa mai inganci, da tabbatar da daidaiton darajar kudaden dake ajiye a waje, a cewar gwamnatin. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)














