Sabbin alkaluman da hukumar kula da kudin musaya ta kasar Sin ta samar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Disamban shekarar 2023 da ta gabata, gaba daya adadin kudin musayar da kasar Sin ta adana ya kai dalar Amurka biliyan 3238, adadin da ya karu da dala biliyan 66 da miliyan 200 bisa na karshen watan Nuwamban bara, wato ya karu da kaso 2.1 cikin dari. Haka kuma ya karu da dala biliyan 110 da miliyan 300 wato kaso 3.5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2022.
Jami’in da abin ya shafa na hukumar kula da kudin musaya ta kasar Sin ya yi tsokaci cewa, adadin kudin musayar Sin ya karu a watan Disamban bara, sakamakon tasirin manufofin kudi na wasu manyan kasashen duniya, kuma tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba yadda ya kamata a halin da ake ciki yanzu, lamarin da zai taimakawa zaman karkon adadin kudin musayar da kasar Sin ke adanawa. (Mai fassara: Jamila)