Yanzu haka adadin matan kasar Sin mamallaka sana’o’i na ta karuwa sannu a hankali, inda ya zuwa yanzu mata ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba mai inganci a kasar.
Wasu alkaluma daga hukumar lura da hada hadar kasuwanni ta kasar sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar bara, adadin kamfanoni da matan kasar Sin suka zuba jari sun haura miliyan 23, adadin da ya kai kaso 41.6 bisa dari cikin jimillar kamfanonin kasar masu zaman kan su.
Alkaluman sun nuna adadin hada-hadar kamfanoni masu jarin matan kasar Sin na ta karuwa, da kimanin kaso 9.8 bisa dari a duk shekara tun daga shekarar 2012, a gabar da karin mata ke kafawa, da zuba jari a kamfanoni daban daban. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp