Alkaluman baya bayan nan da kungiyar kamfanonin kirar motoci na kasar Sin suka fitar, sun nuna yadda tsakanin watannin Janairu zuwa Oktoban bana, adadin motoci masu amfani da sabbin makamashi da aka sayar a kasar ya karu zuwa kusan kaso 40%.
Alkaluman sun nuna karuwar irin wadannan motoci da aka samar a kasar zuwa miliyan 9.779, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 33% a shekara, yayin da adadin su da aka sayar ya kai miliyan 9.75, wato karuwar kaso 33.9% a shekara, inda cikin jimillar wadanda aka sayar adadin motoci masu aiki da sabbin makamashi ya kai kaso 39.6%.
A fannin motocin da aka fitar zuwa ketare kuwa, tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba, Sin ta fitar da motoci miliyan 4.855, adadin da ya karu da kaso 23.8% a shekara. Kuma cikin wannan adadi, adadin motoci masu aiki da sabbin makamashi ya kai miliyan 1.058, adadin da ya karu da kaso 6.3% a shekara guda. (Mai fassara: Saminu Alhassan)