Jimilar sabbin kamfanonin kimiyya da fasaha masu saurin ci gaba a kasar Sin, wadanda jarinsu ya zarce dalar Amurka biliyan 1, ta kai 369.
A cewar wani rahoto da aka fitar jiya Lahadi a Beijing, yayin taron dandalin tattauna batutuwan kimiyya da fasaha na Zhongguancun na shekarar 2024, adadin wadannan kamfanoni a kasar Sin, shi ne ya dauki kashi 1 bisa kashi 4n jimilarsu a fadin duniya.
- Li Qiang Ya Jaddada Muhimmancin Gina Tsarin Samar Da Ababen Hawa Masu Aiki Da Sabbin Makamashi Hade Da Na’urori Masu Basira
- Xi Jinping Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken
Masana sun bayyana cewa, a shekarun baya-bayan nan, karfin kasar Sin a bangaren kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na ci gaba da karuwa. Kuma kasar ta karfafawa adadi mai yawa na sabbin kamfanonin kimiyya da fasaha, wadanda ke samar da karin kuzari ga manufar raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi.
Yanzu haka, kamfanonin 369 dake kasar Sin sun shafi bangarori 16, inda na kirkirarriyar basira wato AI da bangaren samar da kananan na’urorin laturoni na Chip ke kan gaba.
Ta fuskar wuraren da suke da mazauni kuwa, akwai wadannan kamfanoni a birane 47 dake fadin kasar Sin, inda sama da kaso 60 suke biranen Beijing da Shanghai da Guangzhou da Hangzhou. (Fa’iza Mustapha)