ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

by Rabi'u Ali Indabawa
10 months ago
Kebbi

Hedkwatar ’Yansanda ta Jihar Kebbi ta kama wani da ake zargin dan ta’adda ne a yankin Illo, cikin Karamar Hukumar Bagudo ta jihar.

Haka kuma, rundunar ta kwato bindigogi biyu na gida da harsasai guda hudu a wani samame da aka kai bisa sahihan bayanan sirri.

  • Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko
  • Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar a ranar Talata.

ADVERTISEMENT

Abubakar ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 9 ga Nuwamba, 2025, bayan wani sumame na gaggawa da Dibisional Police Officer (DPO) na Illo ya jagoranta bisa bayanan sirri masu inganci.

Ya ce an gudanar da aikin tare da hadin gwiwar ’yan sa kai a kauyen Tungar Gwani, inda aka kama wanda ake zargin mai suna Buba Garba, dan shekara 27, mazaunin kauyen Takalafiya da ke Karamar Hukumar Suru.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

“Da zarar wanda ake zargin ya hango jami’an, ya yi amfani da wuka ya yanki daya daga cikin ’yan sa kai a kugu da hannu, wanda hakan ya jikkata shi sosai,” in ji mai magana da yawun ’yansandan.

Ya kara da cewa an garzaya da dan sa kai da ya ji rauni zuwa cibiyar lafiya mafi kusa, inda yake karbar magani a halin yanzu.

Bayan binciken jiki da aka yi wa wanda ake zargi, jami’an sun samu bindiga daya ta gida, bindiga daya, da kuma harsasai guda hudu a hannunsa.

A cikin martaninsa, kwamishinan ’yansandan jihar, CP Bello Sani, ya yaba da kwararrun ayyuka da dabarun binciken bayanan sirri da kuma hadin kai tsakanin DPO na Illo da tawagarsa tare da ’yan sa kai na yankin.

Ya ce, “Ina yabawa da yadda sashen Illo suka yi aiki cikin gaggawa da hadin kai. Wannan aikin ya nuna cewa idan hukumomin tsaro da al’umma suka hada kai, masu aikata laifi ba za su samu damar tserewa ba.”

Haka kuma, kwamishinan ya umurci a mika shari’ar zuwa sashen binciken masu laifi (SCID) na jihar da ke Birnin Kebbi domin ci gaba da bincike mai zurfi, da nufin gano cibiyar hadin gwiwar wanda ake zargi da yadda yake gudanar da ayyukansa, tare da kamo abokan aikinsa.

Ya ce, “’Yan sanda kadai ba za su iya cin nasara a wannan yaki ba. Muna bukatar ci gaba da samun goyon bayan jama’a ta hanyar bayar da bayanai cikin lokaci da kuma sahihai.”

Rundunar ta kuma tabbatar da aniyarta wajen kara kaimi a yaki da ’yan bindiga da sauran nau’o’in laifukan tashin hankali a fadin jihar, tare da tabbatar wa jama’a cewa an dauki matakan rigakafi domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

idan za a tunawa a watan Oktoba, jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da kasancewa ’yan kungiyar ’yan bindiga.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa an kama su ne yayin wata hadin gwiwar sumame da jami’an Anti-Kidnapping Skuad da na Sashen Shanono Dibision suka gudanar da misalin karfe 2 na safe, bayan samun sahihan bayanai daga mazauna kauyen Farin Ruwa a Karamar Hukumar Shanono.

Ya kara da cewa ana zargin wadanda aka kama suna hadin gwiwa da ’yan bindigar da ke kokarin shiga cikin Jihar Kano, inda ya bayyana cewa an fara bincike domin gano tsarin hadin gwiwarsu da kuma kama sauran mambobin kungiyar.

Kebbi
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.