Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta bayyana cewa adadin wadanda suka mutu a hatsarin kwale-kwale a ranar Lahadin da ta gabata a unguwar Dabi da ke karamar hukumar Ringim ya kai mutum bakwai.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN), ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wani kwale-kwale mai dauke da fasinjoji 13 a kan hanyarsu ta zuwa ziyarar jaje ya kife bayan ya bugi wani abu.
- Bikin Tsakiyar Kaka Na 2022 Da CMG Ya Nuna Ya Samu Yabo Sosai Daga Masu Kallo A Gida Da Waje
- Yadda Ake Rubutu Da Word (WPS Office) A Wayar Hanu (II)
Rundunar ‘yansandan bayan samun rahoton ta kaddamar da aikin bincike da ceto a wurin tare da taimakon masu ruwa da tsaki a yankin.
Rundunar ‘yansandan ta ce, ta yi nasarar ceto mutane bakwai a nan take wanda aka garzaya da su babban asibitin Ringim domin kula da lafiyarsu.
Biyu daga cikin mutane bakwai da aka gano, Bara’atu Garba mai shekaru 30 da Mahmud Surajo mai shekaru 3, likitocin da ke bakin aiki su tabbatar da mutuwarsu.
An kwantar da sauran mutane biyar a asibiti, yayin da sauran shidan da suka jikkata ba a gansu ba.
Kakakin rundunar, DSP Lawan Shiisu, a wata sanarwa da ya fitar a Dutse a ranar Litinin, ya tabbatar da samun karin gawarwakin mutane biyar, wanda ya kawo adadin mutanen da suka mutu a lamarin zuwa bakwai.
“Daga cikin mutane shida da suka bace a hatsarin kwale-kwalen jiya a karamar hukumar Ringim, rahoton ya nuna cewa an sake gano wasu gawarwaki biyar yayin da mutum daya ya bace.
“Ya zuwa yanzu mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a lamarin,” in ji kakakin.
Shiisu ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin ceto sauran mutanen.