Jam’iyyar hadaka ta ADC ta bukaci Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihohin Katsina da Zamfara sakamakon karuwar rashin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da rayuka 140 a cikin watannin biyu da suka gabata.
A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya Sanya wa hannu a kai, jam’iyyar ta bayyana kashe-kashen a matsayin wata shaida da ke nuna cewa an samu gagarumar baraka a cikin harkokin tsaron Nijeriya, sannan ta soki gwamnatin tarayya kan kasa shawo kan lamarin.
- Sin: Shawarar Gina Kyakkyawar Makomar Bil Adam Ta Bai Daya Ta Samu Amincewa A Duniya
- Marafa Ya Fice Daga APC, Ya Zargi Tinubu Da Watsi Da Zamfara
ADC ta yi Allah wadai kan kisan gilla da aka yi kwanan nan a Malumfashi da ke Jihar Katsina, inda aka tabbatar da cewa an harbe masallata har 30 a masallaci da kona mutum 20 da ransu da kuma gidajensu. Haka nan ta bayyana cewa an sake kashe mutum 47 a Zamfara, ciki har da mutum 38 duk da an biya kudin fansa.
“Wannan mummunan aikin yana nuna gazawar harkokin tsoro da ‘yan Nijeriya suke fuskanta a karkashin wannan gwamnati ta APC. Kazalika, yana zama manuniya kan tabarbarewar rashin tsaro a kasarmu, wanda ya sa har babban jami’in tsaro na kasa ya yi kira ga ‘yan kasa su koyi kare kansu,” in ji Abdullahi.
Jam’iyyar ta kuma caccaki Shugaba Tinubu kan burus da abubuwan da suka fi muhimmanci, ta zarge shi da mayar da hankali kan al’amuran da suka shafi kasa da kasa mai makon magance rikicin da al’ummar kasar nan ke fuskanta.
“Abin takaici ne cewa maimakon fuskantar wadannan mummunan lamuran da wahalar da suka jawo, shugaban kasa Tinubu na ci gaba da tafiya kasashen waje, yana holewa a kasashen ketare, yayin da ‘yan kasa ke mutuwa da yawa,” in ji sanarwar.
ADC ta sake ja kunnen gwamnan jam’iyyar PDP kan gudanar da taron siyasa a Jihar Zamfara kanaki kadan da kiyan mutane masu dimbin yawa.
“Maimakon tsayawa cikin hadin kai tare da abokin aikinsu da al’umma, sun gudanar da gangamin siyasa a garin da har yanzu ke fama da kisan gillar jama’a. Abubuwan da suka gudana a wurin taron na daukar hotunan cikin murna bai nuna cewa sun damu da kasan kiyashi da aka yi wa al’umma a jihar ba, “in ji jam’iyyar.
Baya ga kiran saka dokar ta bacin, jam’iyyar ADC ta bukaci a sake duba tsarin tsaron kasar nan gaba daya.
“Shawarar da babban hafsan tsaro ya bayar ga ‘yan kasa kan su kare kansu, wata alama ce da ke nuna cewa tsarin tsaron kasar nan na buktar sake sabunta shi cikin gaggawar,” in ji ta.
Jam’iyyar ta kammala da zargin jam’iyyar APC da PDP kan fifita siyasa sama da jin dadin ‘yan Nijeriya.
“APC da PDP ba su damu da jin dadin al’ummar Nijeriya ba. Su dai sun fi nuna sha’awarsu ga samun shugabanci a cikin harkokin siyasa, inda idanunsu ke rufewa wajen ganin irin wahalhalu da kunci da ‘yan Nijeriya ke fama da su,” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp