Jam’iyyar ADC ta gargaɗi Gwamnatin Tarayya da ta guji amfani da zargin yunƙurin juyin mulki da ya shafi wasu sojoji a matsayin hujja don murƙushe ‘yan adawa ko masu sukar gwamnati.
A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce tana ɗaukar duk wata barazana ga tsarin dimokuraɗiyya da muhimmanci, amma tana nuna damuwa kan yadda ake amfani da irin waɗannan zarge-zarge don cimma manufofin siyasa.
- Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya
- Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo
Jam’iyyar ta ce tana bibiyar rahotannin da ke danganta wasu sojoji da aka kama da zargin yunƙurin juyin mulki, da kuma jita-jitar cewa wani tsohon gwamna daga kudancin ƙasar na fuskantar bincike bisa zargin tallafa wa waɗanda ake tuhuma.
“Ko da yake muna adawa da duk wani yunƙuri da zai rushe tsarin mulki, abin damuwa shi ne yadda ake iya amfani da irin wannan zargi wajen farautar ‘yan adawa da masu sukar gwamnati,” in ji sanarwar.
ADC ta kuma zargi gwamnati da yin shiru kan batun, tana mai cewa wannan na iya zama dabara ta karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin da ƙasar ke fuskanta, musamman a fannonin tattalin arziƙi da shugabanci.