Jam’iyyar ADC ta yi Allah wadai da rufe gidan rediyon Badeggi 90.1 FM da ke Minna da Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya yi.
Jam’iyyar ta bayyana cewa, hakan ya nuna yadda ake kama karya a bangaren zartarwa, ta hanyar watsi da ‘yancin da tsarin mulki ya bayar, da kuma yadda ake ci gaba da ruguza ka’idojin dimokradiyya a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.
- Gwamnatin Katsina Ta Gabatar Da Matsayarta A Taron Jin Ra’ayiyin Jama’a
- Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa matakin da Gwamna Bago ya dauka na rufe gidan rediyon Badeggi FM “da sauri” ba komai ba ne illa cin zarafi ga ‘yancin ‘yan jarida da kuma taka doka karara kamar a tsarin mulkin kama-karya na sojoji.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar ta damu matuka da abin da ya kira dabi’ar kama-karya a tsakanin gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki.
ADC ta bukaci majalisar dokokin kasar da ta dauki matakin gaggawa don karfafa ‘yancin cin gashin kai na hukumar kula da kafofin yada labarai (NBC) tare da killace ka’idojin yada labarai daga tsoma bakin ‘yan siyasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp