A kowace shekara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON tana kayatarwa ta hanyar kafa tarihi da kuma abubuwan mamaki da ake yi a gasar. Sai dai gasar da aka yi wadda aka buga a kasar Kamaru wadda kasar Senegal ta lashe ita ce gasar da aka buga da aka samu karancin zura kwallaye a raga, inda aka zura kwallo 100 cif.
Amma a wannan gasar wadda ake bugawa a kasar Ivory Coast, gasar ta zama ta daban duba da irin abubuwan da suka faru.
- AFCON 2023: Za A Kece Raini Tsakanin Nijeriya Da Cote de’Voire A Wasan Karshe Ranar Lahadi
- Yadda Nijeriya Ta Taka Rawar Gani Har Zuwa Zagayen Karshe Na Gasar AFCON
Gasar AFCON 2023 da ake yi yanzu ita ce gasar da aka fi zura kwallo a raga cikin shekaru 13 da suka gabata.
Daya daga cikin dalilan da yasa aka zura kwallaye a raga a wannan lokacin shi ne; yanayin yadda kwallon kafa ya canja a duniya, kowa yana kokari wajen kai hari domin samun nasara. Kasashe da yawa da suka halarci gasar ta bana sun mayar da hankali ne wajen neman hanyar zura kwallo a raga ta hanyar samar da hanyoyin cin kwallaye.
Bugu da kari, kwarewar yan wasan gaba daga kasashen daban-daban ya samar da hanyoyin zura kwallo a raga saboda an samu kwararrun yan wasan gaba a wannan shekarar.
Sannan yadda masu horar da kasashen suma suka dukufa wajen nemo hanyoyin zura kwallo a raga ya taimaka kasancewar an samu canje-canje a duniya musamman wajen shirya yadda za a ci kwallo.
MANYAN ‘YAN WASA SUN KASA KOMAI
Manyan ‘yan wasa da ake ganin tauraruwarsu za ta haska sun kasa tabuka abin azo a gani, wanda hakan yasa da yawa daga cikin manyan kasashen su suka kasa yin nisa a gasar saboda gazawar manyan ‘yan wasan wajen fitar da su kunya.
Manyan ‘yan wasan da suka gaza tabuka abin azo a gani a kasashen su sun hada da Mohamed Salah da Riyad Mahrez da Achraf Hakimi da Mohamed Kudus da dai sauran su.
Kazalika, dan wasa, Victor Osimhen na Nigeria, shi ne kusan jagoran tawagar ‘yan wasan duk da cewa ba shi ne kaftin ba, amma kusan shi ne wanda yake karfafa guiwar ‘yan wasa a cikin fili, sannan kasancewarsa gwarzon dan wasan Afirka yasa ana ganin ya zama kashin bayan tawagar.
Sai dai duk da haka, kwallo daya kacal ya iya zura wa a raga tun wasan farko sai, dai zai yi fatan ganin ya zura kwallo a wasan karshe.
Sakamakon gazawar manyan ‘yan wasa da kasashen su a gasar ta bana, an samu kasashe da ‘yan wasan su kuma tauraruwarsu ta haska, kamar tawagar ‘yan wasan kasar Cape Verde, musamman dan wasan su na baya Logan Costa, mai shekara 22 a duniya.
Sai dan wasan gaba na Equatorial Guinea, Emilio Nsue, wanda ya zura kwallo uku rigis a wasa daya a cikin rukuni, kuma rabon da a samu dan wasa ya zura kwallo uku a wasa daya tun shekara ta 2008. Sannan har ila yau, shi ne dan wasan da yafi zura kwallo a gasar bana, inda yake da kwallaye biyar.
Sai wanda ya nuna wata bajintar, mai tsaron ragar Afirka ta Kudu, kuma kaftin ɗin tawagar, Ronwen Williams, wanda ya kafa tarihin mai tsaron ragar da ya buge bugun daga kai sai mai tsaron raga guda hudu a wasa daya. A wasan da suka doke kasar Cape Verde.
Wasan karshe da za a buga a gobe Lahadi 11/02/20224, zai kasance mai zafi domin mai masaukin baki za ta yi fatan lashe kofin yayin da Nigeria ma za ta yi kokarin ganin ta dawo gida da kofin.