Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Nijeriya (Super Eagles), ya lashe kyautar dan wasan da ya fi kokari a gasar duk da cewar Nijeriya ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun masu masaukin baki da ci 2-1.
Ekong ya taka rawar gani sosai da ya taimakawa Nijeriya kaiwa wasan karshe a gasar, inda ya jefa kwallaye uku a raga ciki har da wadda yaci Cote de’Voire a wasan karshe da aka buga ranar Lahadi.
Dan wasan na PAOK da ke kasar Girka ya doke manyan ‘yan wasa da suka hada da Yannick Kessie, Percy Tau da sauran su wajen lashe wannan kyauta ta gwarzon dan wasan kofin kasashen Afirika na bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp