Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matukar farin cikinsa da yadda tawagar kwallon kafa ta Nijeriya ta taka rawar gani a gasar kofin kasashen Afirika da aka kammala a kasar Cote de’Voire.
Tinubu ya bayyana haka ne ta bakin babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale a safiyar yau Litinin.
- AFCON 2023: Muna Alfahari Da ‘Yan Wasan Super Eagles -Tinubu
- AFCON 2023: Shettima Ya Je Ivory Coast Don Kallon Wasan Super Eagles Da Afrika Ta Kudu
“Ina matukar alfahari da ‘yan wasa da jagororin tawagar Super Eagles, a kan yadda suka yi aikin tukuru wajen ganin sun daga martabar Nijeriya a harkar kwallon kafa ta hanyar zamo wa na biyu a babbar gasar da aka kammala” Cewar Tinubu.
Daga karshe ya bukaci yan wasan da su kara jajircewa wajen ganin martabar Nijeriya ta dawo a fagen kwallon kafa a Afirika da ma Duniya baki daya.