Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya da Jose Peseiro zai jagoranci tawagar a yau Asabar yayin da za su buga wasansu na farko a gasar cin kofin duniya na kasashen Afirika ta bana da aka fara a kasar Cote d’Voire.
Duk da cewar Peseiro ya zabi ‘yan wasa 25 zuwa kasar Cote d’Voire, uku daga cikinsu da suka hada da Ndidi da Boniface da Sadiq Umar sun samu rauni yayin daukar horo, wanda hakan ya tilasta maye gurbinsu da Yusuf Alhassan da Teran Moffi da kuma Paul Onuachu a cikin tawagar.
- AFCON 2023: ‘Yan Wasan Da Za Su Haskaka A Gasar Kofin Afirka
- AFCON 2023: Ma Su Masaukin Baki Sun Doke Guinea Bissau Da Ci 2-0
Ana saran Peseiro zai fara wasansa na yau da yan wasa kamar haka
Mai tsaron raga: Francis Uzuho
Masu tsaron baya: Omeruo da Ajayi da Ekong da kuma Zaidu.
‘Yan wasan tsakiya: Iwobi da Aribo da Yusuf.
‘Yan Wasan gaba: Lookman da Simon da kuma Osimhen.