Yayin da ake ta shirye-shiryen karawa tsakanin ƙungiyar Super Eagles ta Nijeriya da Elephants ta Ivory Coast a wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Afirka na bana (AFCON 2023), tuni Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar Da da Kai ta Ƙasa (NOA) ta fara gangamin tara wa ‘yan wasan Nijeriya ɗimbin magoya baya a dukkan jihohin ƙasar nan.
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce ma’aikatarsa za ta raba wa jama’a dubunnan tutocin Nijeriya a wuraren kallon ƙwallon ƙafa a faɗin ƙasar nan.
- AFCON: Mai Yi Wa Kasa Hidima Ya Rasu Yayin Kallon Wasan Nijeriya Da Afrika Ta Kudu A Adamawa
- AFCON 2023: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Gwamnatin Nijeriya Zuwa Kallon Wasan Karshe
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Ministan, Malam Rabi’u Ibrahim ya fitar, ya ce tuni NOA ta fara wannan gagarumin aikin domin ɗabbaƙa ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi a shirin farfaɗo da kishin ƙasa a zukatan ‘yan Nijeriya.
Ya ce hakan kuma wani hoɓɓasa ne da zai ƙara wa ‘yan wasan Nijeriya ƙwarin gwiwar kaiwa ga nasarar ɗaukar kofi.
Za a buga wannan wasa a yau Lahadin a Dandalin Alassane Quattara da ke Abidjan, babban birnin Ivory Coast, ƙasar da ta ɗauki baƙuncin shirya gasar.
Idris ya ce, “Tutar ƙasa na ɗaya daga cikin tambarin da kowace ƙasa ke tutiya da shi, domin ita ce madubin hangen nesan shirin wannan gwamnati na wayar da kai da cusa ɗa’a da kyawawan ɗabi’u a dukkan al’amurran tafiyar da rayuwar mu.
“To, yau babbar rana ce da mu ka samu muhimmiyar damar nuna wannan kishi da kuma kyakkyawan ƙudiri na wannan gwamnatin ga ‘yan Nijeriya.”
Ministan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya mazauna Ivory Cost cewa su yi fitar farin ɗango zuwa filin wasan domin nuna wa ‘yan wasan mu goyon baya da kuma nuna kishi ga ƙasa.
Ya ce Shugaba Bola Tinubu ya gamsu sosai da irin takun wasan da Super Eagles su ka yi a yayin karawar su da ƙungiyoyin ƙasashe daban-daban.
Ya ce kuma ya na da ƙwarin gwiwar cewa nasara na tare da Nijeriya.
Ya ce: “Gwamnati na da ƙwarin gwiwar cewa ‘yan wasan Super Eagles ne za su yi nasarar ɗaukar kofin na AFCON, wanda hakan zai kasance na huɗu kenan da Nijeriya za ta ɗauka. Kuma duk wani irin goyon baya da buƙatun da ƙungiyar ta nema, tuni ta samu daga gwamnati, domin dai a ƙarfafa masu gwiwa don kaiwa ga nasarar ɗaukar Kofin Afrika.”
Kafin Nijeriya ta kai ga wasan ƙarshen na yau dai sai da ta lallasa Afrika ta Kudu da ci 4:2 a bugun daga kai sai gola, a wasan kusa da na ƙarshe, bayan an tashi wasan 1:1.
Wannan nasara da Nijeriya ta samu, ta ƙara wa ‘yan ƙasa karsashin kishi a zukatan su sosai.