Kasar da ta lashe gasar kofin nahiyar Afirka na 2023 da za a yi a kasar Cote d’Ivoire za su dawo gida da tukuicin dala miliyan 7 kwatankwacin Naira biliyan 6.53 kamar yadda hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta sanar da karin kashi 40 na kudin tukuicin gasar.
An kara kudin tukuicin ne daga dala miliyan 5 zuwa 7 da aka bai wa Senegal saboda lashe gasar ta shekarar 2021 a Kamaru.
- Rundunar Soji Ta Kudancin Sin Ta Gudanar Da Ayyukan Sintiri Na Dakarun Sojin Ruwa Da Na Sama A Tekun Kudancin Kasar
- Kakakin MOFA: Abin Da Duniya Ke Bukata Shi Ne Hadin Kai
Kasar da ta zo na biyu a gasar a Cote d’Ivoire 2023, za ta samu dala miliyan 4, yayin da biyun da suka zo mataki na kusa da karshe za su samu dala miliyan 2.5 kowanne. Sai kuma kasashen da suka fafata a zagayen kwata fainal za su samu dala biliyan 1.3 kowannensu.
Shugaban hukumar CAF, Dr Patrice Motsepe, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an samu karin kudaden kyautar biyo bayan ci gaban da aka samu cikin shekaru biyu da suka gabata a gasar.