Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, a bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, zai jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin halartar wasan karshe na gasar kofin kasashen Afirika, inda Nijeriya za ta buga da kasar Cote de’Voire.
Kashim Shettima, ya halarci wasan kusa da na karshe wanda Nijeriya ta samu nasara a kan kasar Afirika Ta Kudu a ranar Laraba a filin wasa na Le Paix da ke Bouke.
Ana ganin cewar halartar manyan jami’an Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a filin wasa na Alassane Outara a ranar Lahadi zai karawa ‘yan wasan kasar kwarin guiwar lashe kofin a karo na hudu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp