Kamar yadda aka tsara, tuni aka fara gasar cin kofin Afirka a ranar 13 ga watan Janairu aka fara gasar cin kofin Afirka karo na 34, kuma za a kammala ranar 11 ga watan Fabrairu a kasar Ibory Coast, wadda ita ce mai masaukin baki.
Sai dai gasar ta wannan karon za ta samu bakuncin zakakuran ‘yan wasa da tauraruwarsu take haskawa a duniya kuma sun buga wasanni a gasar a shekarun baya kuma har yanzu suna haskawa.
- Jihar Kaduna Za Ta Ƙarfafa Ƙawancen Tattalin Arziki Da Ƙasar Jamus
- Kasar Sin Ta Harba Kumbon Dakon Kaya Domin Aikewa Da Kayayyaki Ga Tashar Sararin Samaniya
Fitattun ‘yan wasan nahiyar Afrika da suka yi fice a duniya sun fara baje-koli, tun daga ranar 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairu, LEADERSHIP HAUSA ta zakulo ‘yan wasan da tauraruwarsu ta fara haskawa.
Sadio Mané (Senegal)
Mane shi ne dan wasan da ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na 2022 kuma dan wasan na tawagar Senegal zai sake fitowa idon duniya a wannan gasar, wadda kasarsa za ta yi yunkurin kare kambunta da zimmar komawa da shi gida.
Duk da yake, ya bar nahiyar Turai zuwa kasar Saudiyya da kwallo, Sadio Mane bai rasa kwarewarsa da zafin namansa ba ko kadan sannan shi ne hasken tawagar Senegal, kuma ba shi da burin da ya wuce lashe gasar karo na biyu a jere.
Bincent Aboubakar (Cameroon)
Yawanci a wasannin gasa mai yawa shi ne yake goya tawagar Kamaru a kafadarsa domin Bincent Aboubakar shi ne kyaftin din Kamaru kuma wanda ya fi ci musu kwallo a ‘yan shekarun bayan nan.
Kwarin gwiwarsa da kyakkywan fatan da ya ke da shi da kuma kwarewarsa a jagoranci su ne za su kan Kamaru ga nasarar lashe gasar karo na shida a tarihi kamar yadda suke fata.
Sébastien Haller (Côte d’Iboire, 30)
Karo na biyu kenan da zai buga gasar Afcon, ba shi da wani buri da ya wuce buga wannan gasa a gida gaban magoya bayan da suka karbe shi hannu biyu-biyu.
Sébastien Haller mai shekara 30 ya kai wata matuka da ake tsammanin zai nuna kansa a wannan gasa kamar yadda yake yi a nahiyar Turai.
Mohamed Amoura (Algeria)
A lokacin da manyan ‘yan wasan suka mamaye tawagar Algeria irinsu Mahrez Feghouli Slimani da sauransu, sabbin matasa irinsu Mohamed Amoura za su so a gabatar da su a matsayin sabbin fuskar gasar shekara ta 2023. Kuma hankali zai koma kansu muddin aka basu dama suka yi amfani da ita.
Matashin dan wasan tsakiyan, ya nuna kansa a kungiyarsa ta Belgium na tsawon kusan shekaru biyu, kuma ya taimaka wa kasarsa wajen kai wa ga manyan gasanni a ‘yan shekarun nan.
Bictor Osimhen (Nigeria)
Tawagar Super Eagles ta Nigeriya ta dade ba ta yi shahararren mai zura kwallo a raga ba kamar dan wasa Bictor Isimhen tun bayan marigayi Rasheed Yakini, kuma abu ne mai wahala ka fitar da wannan jerin sunaye babu gwarzon nahiyar Afrika na 2023.
Bictor Osimhen da ya zama gwarzo na bayan nan, ya sake samun daukaka a wasannin kwallo a nahiyarmu ta Afirka kuma shi ne yake jan ragamar tawagar Nijeriya, kuma hankali ya karkata kansa a Cote d’Iboire domin ganin rawar da zai taka.
André Onana (Cameroon)
A halin yanzu ga masu Kallon kwallon kafa a duniya, sunan mai tsaron ragar Kamaru da yake jan ragamar jaridu a nahiyar Turai kusan ko wane mako, saboda abin da yake kokari ko akasin haka a kungiyarsa ta Manchester United. Sai dai an fuskanci tazgaro da turjiya bayan da Manchester United ta bukaci mai tsaron ragar ya zauna ya buga wa kungiyar wasan da suka tashi 2-2 da kungiyar Tottenham a filin wasa na Old Trafford.