Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF ta sanar da raba jadawalin gasar cin kofin Afirka da za a gudanar a bana a kasar Morocco inda tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya ta fito a rukuni na C da ya hada da kasashen Tunisia sa Uganda da kuma kasar Tanzania. A bikin da ta gudanar a Mohammed B National Theatre a birnin Rabat ranar Litinin, bikin ya kunshi tawaga 12 da aka raba su rukuni shida dauke da hurhudu kowanne.
Tun a cikin rukunin da akwai wasannin da za su yi zafi kuma na hamayya da suka hada a fafatawa tsakanin Moroccco da Mali da na Nijeriya da Tunisia. Wadannan wasannin suna da tarihi sosai a gasar cin kofin nahiyar Afirka kuma ana ganin suna daya daga cikin manyan wasannin da za a zubawa ido domin ganin yadda za ta kasance musamman a wasannin cikin rukuni.
- Gwamna Radda Ya Samar Da Keke Napep Don Saukaka Zirga-zirga A Katsina
- An Samu Ci Gaba A Bangaren Kayayyakin Da Sin Ta Fitar Zuwa Kasashe Da Yankuna 160 A 2024
Sauran manyan wasannin da za su dauki hankalin masu kallo sun hada da karawa tsakanin Senegal da Jamhuriyar Congo da na Algeria da Burkina Faso da na Cote d’Iobire da Kamaru. Sannan kamar yadda aka tsara gasar, za a fara da bude labulen babbar gasar ta Afirka a wannan shekarar ta 2025 da wasa tsakanin mai masaukin baki, Morocco da Comoros a birnin Rabat.
Har ila yau, za a fara gasar cin kofin Afirka daga ranar 21 ga watan Disambar 2025 zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2026 kamar yadda hukumar dake kula da wasannin nahiyar Afirka ta CAF ta tsara.
Yadda aka raba jadawalin AFCON 2025:
Rukunin farko: Morocco, Mali, Zambia, Comoros — Rukuni na biyu: Egypt, South Africa, Angola, Zimbabwe—- Rukuni na uku: Nigeria, Tunisia, Uganda, Tanzania
Rukuni na hudu: Senegal, DR Congo, Benin, Botswana
Rukuni na biyar: Algeria, Burkina Faso, Ekuatorial Guinea, Sudan
Rukuni na shida: Cote d’Iboire, Cameroon, Gabon, Mozambikue