An tabbatar da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Royal Antwerp ta kasar Belgium Alhassan Yusuf a matsayin wanda zai maye gurbin Wilfred Ndidi a cikin tawagar Nijeriya a gasar cin kofin Afrika na 2024.
Yusuf wanda tun farko yana cikin yan wasan da aka fitar na wucin gadi ta Super Eagles mai mutum 41, ana sa ran zai iske takwarorinsa a sansaninsu na Abu Dhabi, UAE a ranar Laraba.
- Sin Ta Kaddamar Da Kidaya Ta Kasa A Fannin Tattalin Arziki
- Matatar Dangote Ta Karbi Danyen Mai Karo Na 4 Daga NNPC
Wannan dai shi ne karon farko da dan wasan ya samu kira domin wakiltar Nijeriya.
Ndidi ya samu rauni kafin wasan da Leicester City ta doke Huddersfield Town da ci 4-1 a ranar Litinin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp