Bankin raya kasashen nahiyar Afrika (AFDB) ya sha alwashin tallafa wa bangaren noma a Nijeriya da jarin dala milyan 134 da nufin bunkasa noman kayan abinci.
Shugaban bankin, Akinwunmi Adesina ne, ya bayyana aniyar yayin ziyarar Cibiyar Nazarin Noman Tsandauri ta Jami’ar Bayero da ke Kano.
Adesina, ya kuma jaddada muhimmancin samar wa manoma bayanai a kan noman zamani, musamman ma yanzu da ake fama da kalubalen sauyin yanayi.
Adesina ya bayyana aniyar bankin ta bunkasa ci gaban fasaha a harkar noma.
Ya ce, “Zamu hada kai da cibiyar nazarin noman tsandauri domin inganta ayyukanta a bangaren hasashen yanayi da tattara bayanai, ta haka zamu tallafa wa manoma su gudanar da tsare-tsare yadda ya dace.”
Ya jinjinawa kokarin shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Sagir Adamu Abbas da daraktan cibiyar nazarin noman tsandauri, Jibrin Muhammad Jibrin saboda tallafin da suke bai wa manoma wajen yin amfani da fasaha a harkar noma a irin wannan lokaci da ake yaki da sauyin yanayi.