A jiya ne, cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka wato (Africa CDC) a takaice, ta kaddamar da wani dakin gwaje-gwajen bincike da kasar Sin ta samar a hedkwatarta dake Habasha.
Cibiyar ta bayyana cewa, kammala dakin gwaje-gwajen, wani muhimmin ci gaba ne, a kokarinta na samar da wata cibiyar kula da lafiyar jama’a ta nahiyar, wadda za ta agazawa mambobin kungiyar Tarayyar Afirka (AU) wajen kara gano cututtuka, da sanya ido da kuma matakan dakile barkewar cututtuka.
- Xi Ya Ziyarci Kauyuka Domin Duba Rayuwar Manoma A Yanayin Sanyi
- Kamfanoni Da Dama Sun Amfana Da Baje Kolin CIIE
Manyan jami’ai daga hukumar gudanarwar AU da na cibiyar, da jami’an diflomasiyya na tawagar kasar Sin dake kungiyar AU, da wasu manyan jami’ai ne suka shaida bikin kaddamarwar da ya gudana a harabar hedkwatar cibiyar Africa CDC da ke yankin kudancin Addis Ababa, babban birnin Habasha.
Babban darektan cibiyar Africa CDC Jean Kaseya, ya yabawa gwamnatin kasar Sin, bisa goyon bayan da ta bayar wajen ganin an samar da wani sabon tsarin kiwon lafiyar jama’a da gine-gine a nahiyar Afirka, wanda zai taimaka wajen magance, da gano da kuma tunkarar duk wata barazana ta kiwon lafiyar jama’a a fadin nahiyar. (Ibrahim)