A safiyar ranar 29 ga watan Maris da ya gabata, wasu Sinawa masu yawon shakatawa, sun isa filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Oliver Tambo dake birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu cikin jirgin sama na kamfanin Air China, wannan ne karo na farko da masu yawon shakatawa suka isa kasar ta Afirka ta kudu daga kasar Sin, tun bayan da kasar Sin ta yi gwajin maido da tawagar masu bude ido zuwa ketare, inda hukumar yawon shakatawa ta Afirka ta kudu ta shirya gagarumin bikin maraba da zuwansu a filin jirgin saman.
Babban karamin jakadan kasar Sin dake wakilci a birnin Johannesburg Zhou Yujiang ya bayyana cewa, yawon shakatawa, wani muhimmin bangare ne na cudanyar al’adu tsakanin sassan biyu.
Al’ummomin bangarori daban daban na Afirka ta kudu sun nuna cewa, kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka fi yawan masu bude ido dake zuwa Afirka ta kudu, don haka Sinawa masu yawon shakatawa suna taka babbar rawa kan ci gaban sana’ar yawon shakatawa ta Afirka ta kudu. (Mai fassarawa: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp