Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang wanda ya kai ziyara a hedkwatar AU dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya bayyana cewa, nahiyar Afirka wani babban dandali ne na hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya, amma ba fagen adawa da manyan kasashen duniya ba.
Qin ya bayyana hakan ne ranar Laraba, a yayin ganawa da manema labarai tare da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka AU, Moussa Faki Mahamat a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Da aka tambaye shi game da ra’ayin kasar Sin kan taron kolin Amurka da Afirka karo na biyu, Qin ya ce, Sin da Amurka dukkansu mambobi ne na dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kuma suna da nauyi mai girma na tabbatar da zaman lafiya, da tsaro da ci gaban duniya.
Ya ce, nahiyar Afirka nahiya ce mai tasowa, mai cike da arziki da fata da kuma kuzari. Yana mai cewa, idan ba a samu zaman lafiya da ci gaba a Afirka ba, to, ba za a samu kwanciyar hankali da wadata a duniya ba.
Ya kara da cewa, abin da Afirka ke bukata, shi ne goyon baya da hadin kai, ba nuna adawa ba. Ya ce, babu wata kasa ko wani daidaikun mutum dake da hakkin tilastawa kasashen Afirka karkata ga wani bangare.
Qin ya sake nanata cewa, kasar Sin tana farin cikin ganin duk wata kasa da ke da gaskiya wajen taimakawa Afirka, samun zaman lafiya da ci gaba. (Ibrahim Yaya)