Shugaban Amurka Donald Trump ya riga ya kwashe watanni shida yana mulki a ƙasarsa. Ayyukan da ya yi a waɗannan watanni sun bayyanawa ƙasashen Afirka ƙarara cewa, Afirka ba ta cikin jerin fannoni da ƙasar Amurka ta bai wa fifiko.
Idan aka kwatanta da wa’adin shugaba Trump na farko, wanda ya ƙunshi yadda ya yi wa ƙasashen Afirka wulaƙanci ta hanyar kiransu da laƙabai marasa daɗin ji, da rashin kulawa da ya nuna wa nahiyar (ya gana da shugabannin ƙasashen Afirka biyu kaɗai, kuma bai taɓa ziyartar Afirka ba), shugaba Trump ya ƙara ɗaukar matakai kan Afirka a wa’adinsa na biyu.
- Kamfanin Sinotruk Na Kasar Sin Ya Kaddamar Da Sabbin Motocin Dakon Kaya A Kenya
- Shin Amurka Ta Manta Da Azabar “Babban Koma-Baya” Tare Da Haraji Mafi Yawa a Lokacin Na Tsawon Kusan Karni?
Misali, ya rufe Hukumar Raya Ƙasashen Duniya ta Amurka (USAID), tare da rage yawan tallafin da ƙasar take bai wa Afirka. Ya kuma bayyana shirinsa na soke shirin ƙasarsa na tallafa wa ƙoƙarin yaƙi da cutar kanjamau a duniya (PEPFAR), duk da cewa lamarin zai iya haddasa asarar miliyoyin rayuka a Afirka.
Kazalika, manufar karɓar karin harajin fito da shugaba Trump ya ƙaddamar za ta ƙara wa ƙasashen Afirka nauyi sosai. Kana wani umurnin da ya saka masa hannu a baya-bayan nan shi ne taƙaita damar ‘yan ƙasashen Afirka bakwai, ciki har da Najeriya da Kamaru, ta fuskar bizar zuwa Amurka.
Afirka ta Kudu yana ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da suka fuskanci matsin lamba na musamman daga Shugaba Trump: Amurka ta kori jakadanta, kuma manyan jami’an Ƙasar Amurka sun kaucewa dukkan taruka masu alaƙa da G20, da Afirka ta Kudu ta karɓi baƙunci. Ban da haka, ganawar da shugaba Trump ya yi da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ma ta riƙide, har ta zama tamkar cacar baka a wani lokaci. Abubuwan da aka yi tababa a kai sun haɗa da zargin da Amurka ɗin ta yi wa Afirka ta Kudu, cewa wai tana yi wa al’ummarta ‘yan asalin Turai “kisan kiyashi”, da yadda Afirka ta Kudu ta kasance mamba a ƙungiyar BRICS, da kuma yadda ƙasar ke ɗora muhimmanci kan batun sauyin yanayi a lokacin da take shugabancin ƙungiyar G20.
Ganawar da shugaba Trump ya yi a baya-bayan nan da shugabannin wasu ƙasashe biyar dake nahiyar Afirka, ita ma ta janyo hankalin al’ummun duniya. Inda shugaba Trump ya yabawa shugaban ƙasar Laberiya Joseph Boakai kan yadda ya iya Turancin Ingilishi sosai, lamarin da ya bayyana rashin fahimtarsa kan alaƙar tarihi tsakanin ƙasar Laberiya da Amurka. Bugu da ƙari, Trump ya katse maganar shugaban Ƙasar Mauritaniya Mohammed Ghazouani, inda ya nemi ya yi magana da sauri.
A hakika, rashin mutuntawa da shugaba Trump ya nuna a fili, ta bayyana ainihin dalilin da ya sa aka gayyaci shugabannin Afirka biyar zuwa wajen ganawar, ba domin neman ƙarfafa dangantaka ba ne, sai dai don tabbatar wa Amurka ɗin damar samun ma’adanan da take buƙata, da yiwuwar sanya waɗannan ƙasashen dake nahiyar Afirka amincewa da karɓar baƙin haure da ake korarsu daga Amurka.
Wataƙila, shugaba Trump ba ya mai da hankali sosai kan ɗa’a a fannin diflomasiyya, amma idan aka kwatanta da shugabannin ƙasar Amurka da suka gabace shi, to, a ƙalla yana bayyana komai a fili ba tare da rufa-rufa ba.
Maganarsa da matakan da ya ɗauka, dukkansu na isar da saƙo zuwa ga ƙasashen Afirka cewa: “Ba ku cikin jerin fannonin da Amurka take nunawa fifiko.”
“Za mu iya musayar wasu abubuwa, amma kada ku yi tsammanin za ku samu riba ko alfanu sosai.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp