Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da kakkausar murya, kan harin da aka kai wa tawagar Majalisar Dinkin Duniya mai kiyaye zaman lafiya a jamhuriyyar Afrika ta tsakiya wato MINUSCA a kwanan baya.
MINUSCA ta tabbatar a ran 29 ga watan nan cewa, rukunin sintiri na tawagar ya gamu da harin masu fafutuka da ba a san ko su wanene ba da safiyar ran 28 ga watan Maris a lardin Haut-Mbomou dake kudu maso gabashin Kasar Afrika ta Tsakiya, kuma mamban tawagar dan asalin Kasar Kenya ya rasa rai sanadiyyar harin. Kwamitin ya bayyana juyayin rasuwarsa tare da jajanta wa iyalansa da gwamnati da jama’ar Kenya.
- Wike Ya Musanta Jita-jitar FaÉ—uwa Ta Rashin Lafiya
- Kisan Mummuken Cutar Mashako A Nijeriya Da Sassan Duniya
Sanarwar wadda kwamitin ya fitar jiya, ta nanata cewa, kai wa jami’an kiyaye zaman lafiya hari laifin yaki ne, inda ya yi kira ga vangarori masu ruwa da tsaki da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tabbatar da dokar jin kai ta kasa da kasa.
Ban da wannan kuma, kwamitin ya kalubalanci gwamnatin kasar da ta gudanar da bincike bisa taimakon MINUSCA ba tare da vata lokaci ba, don gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotu, tare da sanar da kasashen da suke tura sojojinsu cikin wannan aiki idan aka samu sakamako.
Dadin dadawa, kwamitin ya zura ido sosai kan rahotannin da aka gabatar masa kan kudade da makamai da wasu haramtattun kungiyoyi suka samar wa masu fafutuka a kasar, tare da jaddada wajibcin karin bincike da dakile wannan barazana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp