• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ahmad Musa Da Shehu Abdullahi Sun Koma Kano Pillars Da Taka Leda

by Abba Ibrahim Wada
1 year ago
Pillars

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta tabbatar da cewa tsofaffin ƴan wasanninta, Ahmad Musa da Shehu Abdullahi sun koma ƙungiyar domin buga kakar wasa ta 2024 zuwa 2025. 

A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Abubakar Isa Ɗandago, ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce ƴan wasan guda biyu sun koma ƙungiyar kuma an kammala musu rijista domin fara buga wasa.

  • Sin Na Yayata Adalci Da Dabarun Warware Takaddamar Cinikayya A Matakin Kasa Da Kasa
  • Nazari Kan Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu (8)

Ahmad Musa, mai shekara 31 a duniya ya buga wasa a kungiyar karo biyu a baya, inda ya wakilci Kano Pillars a kakar wasa ta 2009 zuwa 2010 da kuma shekara ta 2021.

Shehu Abdullahi kuma, dan asalin Jihar Sakkwato, wanda ba shi da kungiya tun shekarar 2023, ya buga wasa a kungiyar a shekara ta 2012.

Zakarun gasar Firimiyar Nijeriya, Rangers international, sun nemi daukar dan wasa Ahmad Musa, sai dai tsohon kyaftin ɗin na Super Eagles ta Nijeriya, ya fi son buga wa Kano Pillars wasa.

LABARAI MASU NASABA

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

A kakar wasan Ahmed Musa ta farko a Kano Pillars a Shekarar 2009, ya lashe kyautar wanda ya fi zura kwallo a raga a gasar Firimiyar  Nijeriya, inda ya kammala gasar da kwallaye 18 Wanda hakan ne ya ja hankalin kungiyar VVV Venlo ta kasar Netherlands ta ɗauke shi.

Sannan ya buga wasa a kungiyoyin CSKA Moscow ta kasar Rasha da Leceister City ta Ingila sai kuma Al Nassr ta kasar Saudiyya.

Ana saran Ahmad Musa da Shehu Abdullahi za su buga wasan Kano Pillars na ranar Lahadi da Sunshines Stars.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
Wasanni

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara
Wasanni

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
Wasanni

Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?

November 2, 2025
Next Post
Yadda Rayuwa Take A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Nijeriya

Yadda Rayuwa Take A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.