Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Super Eagles, ya kamo tarihin da Zidane ya kafa na yawan buga wa kasarsa wasa.
Ahmed Musa – wanda shi ne ya fi kowa buga wa Nijeriya wasa – ya buga wasansa na 108 a karawar da Super Eagles ta doke Guinea-Bissau da ci 1-0 ranar Litinin.
- Karancin Kudi: NLC Ta Dage Yajin Aikinta Zuwa Mako 2
- An Yanke Wa Da Nijeriya Hukuncin Daurin Shekara 4 Saboda Damfara A Amurka
Dan wasan wanda ya fara murza wa Nijeriya kwallo a 2010 na daga cikin tawagar kasar nan da ta lashe kofin kasashen Afirka a 2013.
Da wannan wasa dan wasan ya kamo tarihin da tsohon dan wasan Faransa Zinedine Zidane, da dan wasan Jamus Jurgen Klinsmann da kuma Tim Cahill na Ingila wadanda duka suka taka wa tawagogin kasashensu wasa sau 108.
Dan wasan mai shekara 30 ya zarta Patrick Vieira da Frank Lampard a yawan wasannin da suka taka wa kasashensu wasa
Ahmed Musa ya ci wa Nijeriya kwallo 16, kuma shi ne dan wasan da ya fi kowanne dan wasa zura ke
kwallo a gasar Kofin Duniya, inda yake da kwallaye hudu.
Ya kuma zura kwallo 92 a kungiyoyi daban-daban da ya taka wa leda.