• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Aikin Gina Babbar Mayankar Dabbobi Zai Taimaka Wajen Kara Samar Da Wadataccen Nama A Nijeriya – Minista

by Abubakar Abba and Sulaiman
8 months ago
Mayankar dabbobi

Ministan Ma’aikatar Bunkasa Kiwo, Idi Mukhtar Maiha ya bayyana cewa, aikin gina mayankar dabbobi ta rukunin kamfanonin ABIS da ke Abuja, baya ga taimakawar da za ta yi wajen sarrafa Nama, za kuma ta taimaka wajen samar da ilimi a fadin kasar nan.

Da zarar an kammala aikin mayankar, za ta taimaka wajen kara bayar da dama a bangaren zuba hannun jari tare kuma da tallafa wa mayankar da ke Jihar Legas, wajen sarrafa Naman Shanu 200 a kowace rana da sarrafa Naman Kajin gidan gona 15,000 da kuma sarrafa tan 100 na Kifi.

  • Abin Da Ya Sa Masu Ruwa Da Tsaki Suka Gana Da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur
  • Wakilin Musamman Na Shugaba Xi Zai Halarci Taron Koli Kan Fasahar AI A Faransa

Kazalika, idan an kammala mayankar,  za a iya sarrafa Shanu 1,000 tare da samar da tan daga 400 zuwa 600 na Kajin gidan gona da Awaki 2,000 da Raguna tan 1,000 na Kifi da sauran makamantansu.

Wannan zuba hannun jari na dala miliyan 30, zai samar da ayyukan yi na kai tsaye kimanin 1,000, tare kuma da samar da ayyukan yi wadanda ba na kai tsaye ba, sama da 20,000 a fannin kiwo a wannan kasa.

Maiha, a jawabinsa lokacin da ya kai ziyarar aiki ga mayankar ta  ABIS da ke yankin Idu a Abuja, ya sanar da cewa; karancin da ake da shi na kwararrun masu kula da fannin kiwon dabobi a kasar, nan ba da jimawa ba; zai zama tarihi.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

A cewar Maiha, kafa wajen bayar da horo da kamfanin na ABIS ya yi, zai cike gibin da ake da shi a fannin kiwo da kuma bayar da gudunmawa wajen kara habaka tattalin arzikin fannin.

Ministan ya kara da cewa, bayar da ingantaccen horo a fannin bunkasa kiwo, zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci da kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar, musamman ma matasa.

Maiha, ya kuma bai wa kamfanin na ABIS tabbacin cewa, ma’aikatarsa, za ta bai wai kamfanin goyon bayan da ya dace, domin samar da kwararru a fannin bunkasa kiwon kasar.

Da yake yin tsokaci kan jajircewa da mayar da hankali na kamfanin na ABIS, Maiha ya bukaci kamfanin ya yi hadaka da ma’aikatarsa, musamman domin cimma burin da ya sanya a gaba na sarrafa Nama a kasar.

Ya kuma jaddada cewa, fannin kiwo na matukar taimakawa wajen samar da ayyukan yi da kuma kara habaka tattalin arzikin kasa.

Shi kuwa a nasa jawabin, Shugaban  kamfanin na ABIS, Jakada Emmanuel Nelson Usman ya bayyana cewa, an kafa kamfanin ne, domin yin amfani da kimiyyar zamani; wajen sarrafa Nama a kasar.

Ya sanar da cewa, ta hanyar kamfanin; za a iya samar da ayyukan yi na kai tsaye da kuma wadanda ba na kai tsaye ba ga ‘yan kasar, wanda hakan zai taimaka wajen kara habaka tattalin arzikin kasar da kuma kara samar da wadataccen abinci a Nijeriya.

Nelson, ya kuma bukaci taimako daga Ministan Ma’aikatar Bunkasa Kiwon, musamman a bangaren sahalewar shigo da sundukan kamfanin da ke dauke da kayan kamfanin ta hanyar tashoshin jiragen ruwa na kasa, musamman don kamfanin ya samu damar kafa makarantar koyar da kiwon dabbobi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

October 11, 2025
Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
Noma Da Kiwo

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

October 11, 2025
Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara
Noma Da Kiwo

Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

October 11, 2025
Next Post
Cinikayyar ‘Yan Kwallon Da Aka Yi A Watan Janairu

Cinikayyar ‘Yan Kwallon Da Aka Yi A Watan Janairu

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Don Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

October 17, 2025
katsina

Tawagar Bankin Duniya Ta Gana Da Gwamnan Katsina Kan Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Muhallinsu

October 17, 2025
Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

October 17, 2025
Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

October 17, 2025
Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

October 17, 2025
Abduljabbar

Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja

October 17, 2025
An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.