Hukumar Alhazai ta kasa, NAHCON ta gargadi al’umma da su guji wani labari da ake yadawa ta yanar gizo cewa, Hukumar za ta dauki ma’aikata.
Gargadin na zuwa ne a wata sanarwa da mataimakiyar daraktan hulda da jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, inda ta aikewa manema labarai a safiyar ranar Alhamis.
- Hukumar Zaɓe Ta Jihar Katsina Ta Ayyana Ranar Gudanar Da Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Jihar
- Nan Da Makonni Uku Ɗalibai Za Su Fara Karɓar Bashi Daga Gwamnatin Nijeriya
Usara ta kuma bukaci jama’a da su yi watsi da batun da ake yadawa kan cewa hukumar za ta dauki ma’aikata.
sanarwar ta kuma nemi jama’a da su bibiyi ingantattun shafukan hukumar don samun ingantattun bayanai game da hukumar NAHCON.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp