• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Aikin Raya Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ya Samar Da Sabbin Damammaki Ga Duniya A Cewar Kusoshin Siyasa Na Kasashe Da Dama

by CGTN Hausa
2 years ago
Ziri Daya

Shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru goma, da kasar Sin ta gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Kuma ya zuwa yanzu, shawarar ta zama sanannen abu da jama’a ke amfani da shi a duniya, tun daga karfafa tushenta har zuwa tabbatar da ita, wadda ta haifar da karfin ingiza ci gaba mai dorewa ga kasashe da dama. 

A yayin da suke zantawa da manema labaru na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin a kwanan baya, a birnin New York na kasar Amurka, kusoshin siyasa na kasashe masu yawa sun bayyana cewa, aikin raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, ya kawo sabbin damammakin samun ci gaba ga duniya, kuma kasashensu na son kara yin la’akari da damar kasuwanci irin ta samun moriyar juna tare da kasar Sin, don inganta matsayin hadin gwiwa.

  • Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Kama Hanyar Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba A Yankin Tsaunin Himalaya
  • Wakilin Sin Ya Yi Karin Haske Kan Ra’ayi Da Matsayin Kasarsa Game Da Yanayin Tsaro Na Kasa Da Kasa Da Kwance Damarar Makaman Nukiliya

Game da hakan, shugaba Julius Maada Bio na kasar Saliyo ya ce, duk wani alkawari da kasar Sin ta yi, ba ta taba gindaya wani sharadi na cika shi ba, kuma shawarar “ziri daya da hanya daya” na da matukar muhimmanci, musamman ta fuskar gina ababen more rayuwa.

Wadannan gine-gine ba wai kawai sun samarwa mutane damar samun hidima daga gwamnati cikin sauki ba ne, har ma sun taimakawa kasarsu wajen samun ci gaban aikin gona ta hanyar kiyaye muhalli, da kuma baiwa kasarsu, da al’ummarsu damar shiga kasuwa yadda ya kamata.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Hassan Shoukry, cewa ya yi sun yi imani manufar dunkulewa da juna ta shawarar “ziri daya da hanya daya”, za ta yi tasiri mai kyau, ciki har da bunkasa cinikayya, da hadin gwiwar kasuwanci, da damar zuba jari da dai sauransu, kuma ci gaba da raya shawarar zai ba da kwarin gwiwa ga Masar, wajen cimma burinta na samun bunkasuwa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

LABARAI MASU NASABA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
Daga Birnin Sin

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Daga Birnin Sin

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Next Post
Gwamnati Tarayya Ta Dakatar Da Shirin N-Power

Gwamnati Tarayya Ta Dakatar Da Shirin N-Power

LABARAI MASU NASABA

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025
Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.