Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya musanta wani bidiyo da ya yadu wanda ke nuna wai ana gudanar da gangamin siyasa don neman goyon bayan takararsa ta shugaban kasa a shekarar 2027. Ya bayyana hakan a matsayin “abu mara ma’ana” da kuma aikin “marasa hankali da masu rudani.”
A wata sanarwa daga daraktan ofishin yada labaransa, Ohiare Michael, an bayyana cewa bidiyon da ake yadawa na daga cikin gangamin da aka gudanar a 2022 kafin zaben shugaban kasa na 2023. Sanarwar ta zargi masu ɓata suna da ƙoƙarin yaudarar ‘yan Nijeriya ta hanyar yada tsohon bidiyo da ƙarya.
- Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi
Sanarwar ta kara da cewa: “Sun jima suna ƙoƙarin ganin sun durƙusar da tsohon gwamnan a kowanne hali, amma sun kasa sau da yawa.” Ta ce waɗanda ke ƙoƙarin ɓata masa suna ba su da wani aikin kirki illa yada ƙarya da rudani.
Ofishin ya ce ba wannan ne karon farko ba da waɗanda suka ƙuduri aniyar ɓata sunan Yahaya Bello ke ƙoƙarin haddasa rikici tsakaninsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Sun bayyana wannan yunkuri a matsayin “wahalalliyar manufa da ba zata yi nasara ba.”
Sanarwar ta kuma jaddada cewa hotunan allon gangamin da ke cikin bidiyon suna ɗauke da kwanan watan 2022, abin da ke tabbatar da cewa wannan labari ƙarya ne da aka ƙirƙira don yaudarar jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp