Aisha, Uwargidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta amince da ikirarin Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai wanda ke zargin wasu a fadar shugaban kasa na yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu zagon kasa.
El-Rufai ya ce, masu yin zagon kasan a Aso Rock ba su wuce wadanda ‘yan takararsu suka sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda kuma har yanzu suna cikin dacin rai.
Aisha ta saka bidiyon ne a shafin Instagram dinta a ranar Laraba, sa’o’i kadan bayan El-Rufai ya yi wannan zargin yayin da ya bayyana a shirin Sunrise Daily na Channels Television.
Uwargidan shugaban kasa, wacce kuma ke jagorantar jirgin yakin neman zaben mata na Tinubu, ta rubuta wannan taken: “#longlivethefederalrepublicofnigeria” a kasan bidiyon da ta wallafa.
El-Rufai ya ce, wadannan mutanen masu yi wa Tinubu zagon kasa, suna fakewa ne da Shugaba Buhari don biyan bukatunsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp